Yanzu-yanzu: Kotu ta yi kwarya-kwaryar hukunci akan zargin rashawa da ake yiwa Ganduje da mai dakinsa

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Wata babbar kotun jihar Kano ta yi watsi da bukar da tsohon gwamnan jihar Kano, kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da wasu mutane bakwai suka shigar inda suke kalubalantar kotun da cewa ba ta da hurumin da za ta saurari karar da ake zarginsu da karbar cin hanci da rashawa.

Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito gwamnatin jihar Kano gabatar da tuhume-tuhume guda 11 da suka hada da cin hanci da rashawa da hada baki da almubazzaranci da dukiyar al’umma da suka kai biliyoyin nairori akan Ganduje da matarsa Hafsat Umar.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Sauran wadanda ake tuhumar sun hada da Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Limited, Safari Textiles Limited, da Lasage General Enterprises Limited.

Alkalin kotun, Mai shari’a Amina Adamu Aliyu, a ranar Talata, a hukuncin da ta yanke, ta yi watsi da bukatar da wadanda ake kara , inda ta ce abun da suka yi kawai suna kokarin kawo tsaiko a shari’ar da ake yi musu ne.

Za mu yi aikin hanyar Utai zuwa Kademi – Shugaban karamar hukumar Wudil

Alkalin ta ce kotun ta na da hurumin sauraron tuhume-tuhumen da aka shigar gabanta a ranar 13 ga Mayu, 2024, a kan wadanda ake kara.

Mai shari’ar ta tabbatar da cewa, ikon gudanar da bincike ba ya rataya a wuyan ‘yan sanda ne kadai ba, ta na mai cewa hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ita ma tana da hurumin gudanar da bincike kan al’amuran da suka shafi laifuka.

Ta bayyana hakan ne a yayin da ta yi watsi da daya daga cikin takardun neman dakatar da shari’ar.

InShot 20250309 102403344

“Ya kamata a ci gaba da shari’ar ko da babu Ganduje da wasu mutane shida. Inji mai shari’a

Ta kuma gayyaci wanda ake kara na shida, Lamash Properties Limited, sannan ta dage sauraron karar zuwa ranar 30 da 31 ga watan Yuli domin sauraren karar.

Solabase

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hakikanin halin da gwamnan Katsina yake ciki, bayan wani hatsari

  Rahotanni daga Katsina na cewa gwamnan jihar Katsina Dikko...

Zargin almundahana: ICPC ku fita daga harkokin Siyasar Kano – Kungiyar Ma’aikatan KANSIEC

Daga Hafsat Abdullahi Darmanawa   Kungiyar ma'akatan wucin gadi da suka...

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...