Hana hirar siyasa kai tsaye: Kungiyar masu maganar Siyasa a gidajen Radio a Kano ta bayyana matsayarta

Date:

Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Kungiyar Gauta Club ta masu maganganun siyasa a kafafen yada labarai a jihar Kano ta bayyana goyon bayanta da matakin da shugabannin kafafen yada labarai suka dauka na dakatar da yada shirye-shiryen iyasa kai tsaye.

“A madadin shugabanni da ‘ya ‘yan wannan kungiya mai albarka ta Gauta Club wadda hadaka ce ta masu gwagwarmayar siyasa a kafafen yada labaru daga jam’iyyu daban-daban a Jihar Kano, muna jaddada goyon bayan mu dangane da matakan da masu ruwa da tsaki su ka dauka domin tsabtace shirye-shiryen siyasa a kafafen yada labarai dake yada shirye-shiryensu a Jihar Kano”.

Shugaban kungiyar Alhaji Hamisu Danwawu Fagge ne ya bayyana hakan lokacin da ya gudanar da taron manema labarai a Kano.

IMG 20250415 WA0003
Talla

“Dakatar da gabatar da shirye-shiryen siyasa kai tsaye da nufin kawo karshen matsalolin da hakan yake haifarwa wanda ya haɗa da cin zarafin masu mutunci, yin kazafi da yin kalamai na ‘batanci da basu dace ba, abu ne da muke goyon bayansa, kuma za mu taimaka wajen samun nasarar wannan mataki”. Inji Danwawu Fagge

Ya ce mataki da masu ruwa da tsaki suka ɗauka ya yi dai dai, domin hakan zai kiyaye mutuncin mutane musamman shugabanni. Matakin kuma zai taimaka wajen kare kafafen yaɗa labarai daga fadawa cikin rikici da hukumomin dake sa ido a kan ayyukansu.

Danwawu Fagge ya jaddada cewa matakin zai ƙara kare waɗanda suke yin hirar daga jefa su kansu cikin laifi kamar yadda dokokin kasa da na yada labarai suka tanada.

“Wannan mataki zai taimaka wajen kare kima da martaba na addinin al’umma da kuma kyawawan al’adunmu da suka had’a da kara, yakana, jin kunya, ganin girman na gaba da sauran kyawawan halayen da aka san mu dasu”.

Zaizayar kasa: Gwamna Abba gida-gida ya raba diyyar Naira Miliyan 600 A Kano

“Kididdiga da Hukumomin dake kula da yaɗa labarai suka fitar na nuni da cewa, Jihar Kano ce a kan gaba wajen sabawa ka’idoji da tanade-tanaden aikin jarida a fannin shirye-shiryen siyasa”. Inji shugaban Gauta Club

“A gaskiya babu wata al’umma da ta san ciwon kanta za ta zuba ido a na yi wa, jama’arta musamman shugabanni da martabar addininta da al’adunta Karan tsaye kuma ta kyale haka ya ci gaba”.

InShot 20250309 102403344

“A saboda haka ne mu kai maraba da wannan mataki na shugabannin kafafen yada labarai na dakatar da shirye-shiryen siyasa kai tsaye, domin hakan zai taimaka wajen tsabtace harshe da kiyayewa wajen cin zarafin masu mutunci. Wannan mataki ya yi dai dai da muradi, da bukatun al”ummar jihar Kano, don haka abin a yaba ne”.

Ya karkara da cewa “A bangarenmu na masu gwagwarmaya a Radiyo da gidajen talbijin, muna nuna cikakken goyon bayan mu tare da yabawa wannan mataki kuma zamu ci gaba da bada goyon bayan ga duk wani matataki na gyara a kowane mataki domin samun kyautatuwar al’amura”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ba da umarnin mayar da Natasha bakin aikinta

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Majalisar...

Yadda Shugabanni da jagororin Jam’iyyar APC na Kano suka kauracewa tarbar Kashim Shattima yayi ziyarar ta’aziyya

Daga Fatima Mahmoud Diso   Shugabanni da jagororin jam'iyyar APC na...

Kotu ta ɗaure wani ɗan Tiktok mai wanka a tsakiyar titunan Kano

    Wata kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya...

Damuna: Mun shirya inganta wuraren tsayarwar motocinmu – Kungiyoyin Direbobin na Kano

Kungiyar matuka motocin kurkura ta jihar Kano da Kungiyar...