Gwamnan Kano ya fidda wasu mata 8 daga gidan yari

Date:

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir ya biyawa wasu mata takwas kudaden bashin da ake binsu wanda ya yi sanadiyyar shigar su gidajen gyaran hali.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24, yace gwamnan ya biya kudin ne yayin wata ziyarar bazata da ya kai gidajen gyaran hali na Goron Dutsen da Janguza.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Gwamna Yusuf wanda ya jajantawa wadanda ke daure a gidan gyaran halin sakamakon ibtilain da tsuka tsinci kanawu a ciki, yace ya kai ziyarar ne domin ganewa idonsa irin yanayi da kuma rayuwar da suke yi a gidan gyaran hali.

Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda yace gwamnati zata samar da tsarin da zata biya kudaden tarar da aka yankewa wasu daga cikin daurarrun domin su tuba su koma ga iyalansu yace gwamnatinsa zata taimaka musu ta hanyar koyar dasu sana’oin dogaro da kai da inganta kula da lafiya da iliminsu.

Zaizayar kasa: Gwamna Abba gida-gida ya raba diyyar Naira Miliyan 600 A Kano

Gwamna Yusuf ya gargadesu da su yi amfani lokutan zamansu a gidan gyaran halin, wajen gyara dabi’u da halayensu, Yana mai cewa gwamnati zata samar da tsarin koyar dasu dasu ilimin addini dana zamani.

Ya yi amfani da ziyarar inda ya kewaya dukkanin sassan gidan kama daga wajen dafa musu abinci da wajen kwanciyarsu tare da duba irin nau’ikan abincin da ake basu.

Ya ja hankalin daurarrun da su yawaita tuba ga Allah tare da Neman yafiya daga iyayensu da kuma yi musu addu’a.

InShot 20250309 102403344

Daya daga cikin daurarrun wanda ya shafe sama da shekaru 30 a daure ya godewa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa wannan ziyara da ya kawo musu.

Wannan ziyara ta gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ta zo daidai lokacin da ake yada wasu korafe-korafe kan yanayin rayuwar da fursunoni su ke ciki a wannan kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Barin jam’iyya bayan ka ci zabe a cikinta babban zunubi ne a Siyasa – Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya...

Nigeria ka iya zama kamar China idan aka koma tsarin jam’iyya daya – Ganduje

  Shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje...

Ba gaskiya a bayanin wasu Manoman Kano da suka ce Muna karbar kudi a wajensu – Civil defense

Rundunar tsaro ta Civil defense ta Kasa reshen jihar...

Korar ma’aikata a Kano: Bashir Gentile ya yiwa Faizu Alfindiki martani mai zafi

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Masanin kimiyar siyasa kuma mai sharhi...