Gwamnatin da ta ke korar Ma’aikata ba ta Cancanci Wa’adi na biyu ba – Faizu Alfindiki

Date:

Daga  Maryam Muhammad Ibrahim

 

Abin takaici ne ganin yadda gwamnatin NNPP a jihar ta dukufa wajen korar ma’aikatan wucin gadi a Hukumar Tara Haraji ta Kano (KIRS).

Wannan mataki na korar ma’aikata a hukumar KIRS ba wai kawai ya jefa su cikin rudani da rashin aikin yi ba ne, har ila yau ya karya zuciyar dubban iyalai da ke dogaro da waɗannan ‘yan uwa don rayuwa.

IMG 20250415 WA0003
Talla

A lokacin da ake bukatar ƙarin tallafi da tabbatar da zaman lafiya a cikin gida da al’umma, sai gwamnati ta zabi wata hanya da za ta ƙara jefa mutane cikin ƙunci.

Matakai 3 da gwamnatin Kano ta dauka kan kafafen yada labarai a jihar

Gwamnatin da ke nuna halin ko-in-kula da rayuwar jama’arta, musamman a lokacin da suka fi buƙatar taimako, ba ta cancanci neman wa’adi na biyu ba. Shugabanci na gaskiya yana tabbatar da walwalar ma’aikata, ba korarsu ba; yana gina ƙasa da gina rayuka, ba rugujewa ba.

InShot 20250309 102403344

Muna kira ga Gwamnatin Kano da ta soke wannan matakin korar ma’aikata wucin gadi, da ta dawo da su bakin aiki, tare da ƙarfafa bangaren haraji domin kara samun kudaden shiga da ci gaba mai dorewa.

Kano tana bukatar gwamnati mai tausayi, mai kare rayuwa, da mai sauraron koke da damuwar jama’a ba wadda ke korar su daga aiki a lokaci mai wahala ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba gaskiya a bayanin wasu Manoman Kano da suka ce Muna karbar kudi a wajensu – Civil defense

Rundunar tsaro ta Civil defense ta Kasa reshen jihar...

Korar ma’aikata a Kano: Bashir Gentile ya yiwa Faizu Alfindiki martani mai zafi

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Masanin kimiyar siyasa kuma mai sharhi...

Sakataren kungiyar NRO Abdulkadir Gude ya rasu

Allah ya yi wa dattijo, kuma Sakataren kungiyar Northern...

Zaizayar kasa: Gwamna Abba gida-gida ya raba diyyar Naira Miliyan 600 A Kano

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...