Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya raba sama da Naira miliyan 600 ga mazauna unguwannin Bulbula da Gayawa wadanda aikin magance da zaizayar kasa ya shafa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24 a ranar Alhamis.

sanarwar ta ce aikin ya kunshi gina ingantattun magudanan ruwa da samar da duk wani abu da magance tare da hana zaizayar kasa a yankin.
Wannan aikin wani yunƙuri ne na ceto garin Gayawa da Bulbula daga mawuyacin halin da zaizayar kasa ta gefa su cikin, kuma aikin hadin gwiwa ne tsakanin gwamnatin jihar Kano da ta tarayya, tare da tallafin bankin duniya.
Matakai 3 da gwamnatin Kano ta dauka kan kafafen yada labarai a jihar
A jawabinsa gwamnan Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa aikin Bulbula da na Gayawa wani gagarumin ci gaba ne ga a gwamnatinsa domin indan an kammala aikin zai dawo da martaba, tsaro da walwala ga al’ummomin yankunan biyu.
“Na yi matukar farin ciki da zuwa na wannan yankin da kaina domin gabatar da takardar biyan diyya ga mutanen da aikin ya shafa a karkashin shirin Resettlement Action Plan (RAP) dake aikin kawar da zaizayar kasa a Bulbula zuwa Gayawa a kananan hukumomin Nasarawa da Ungogo.”
Gwamnan ya bukaci wadanda aka biya diyyar da su yi amfani da kudaden da aka ba su ta hanyar da ta dace, inda ya jaddada biyan diyya ya nuna yadda gwamnatin Abba Gida-Gida ta damu da walwalar ga l’ummarta.
Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin, Jibril Abdullahi Jibril da Fatima Haruna, sun bayyana jin dadinsu ga gwamnatin jihar Kano bisa yadda ta biya su diyyar hakkokinsu.