Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Rahotanni sun tabbatar da cewa Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya fasa fita zuwa gidan gyaran hali na goron dutse kamar yadda aka tsara a yau alhamis.
Wani makusancin fadar sarkin ya shaidawa jaridar Kadaura24 cewa matakin soke fitar ya biyo bayan yadda shugabannin hukumar kula da gidajen gyaran hali na Kano suka je har fada tare da sanarwa sarkin cewa ba su shirya karbar bakuncinsa a wannan ranar ba.
” Mun ga shigowar wasu jami’an hukumar kula da gidajen gyaran hali inda suka shiga suka gana da Sarki Aminu na dan wani lokaci, Ashe fada masu su ka yi cewa ya yi hakuri ya sanya wata ranar domin ziyartar gidan saboda a yau ba su shirya karbar sa ba”.

” Sannan sun fadawa sarkin cewa akwai kyakykyawan zaton a yau gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf zai je gidan gyaran halin don haka suka zo har fadarsa domin ba shi hakuri da neman afuwarsa”. Inji majiyar kadaura24
Ya ce an dan sami turjiya tsakanin Shugabannin hukumar kula da gidajen gyaran halin da wasu cikin manyan hakiman Sarkin, inda wasu suka ce sai an je a haka wasu kuma suke ganin ya kamata sarkin ya hakura da fita tunda Shugabannin gidan sun kawo na su uzurin.
Yadda manoma a Kano suka zargi jami’an Civil defense da karbar kudade a wajensu
Daga karshe da sun sami rahoton Sarkin ya ce ya ya hakura da fitar, kuma tuni an janye motocin Sarkin da aka jera domin fita zuwa gidan gyaran halin na goron dutsu.
Sarkin Aminu Ado Bayero ya shirya zuwa gidan gyaran halin na goron dutsu ne saboda zargin lalata da ake yi da tsakanin Maza da Maza a gidan.
Tuni dai matasan da su ka cika gidan sarkin domin yi masa rakiya suka rarwatse kowa ya kama gabansa.
Idan dai za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito a ranar alhamis din da ta wuce ne sarki Aminu Ado Bayero ya je sauka cikin gari, kuma bayan fitar ne gwamnatin Kano ta gargadi matasa da suke yiwa Sarkin rakiya da su daina bari ana rudarsu.