Kungiyar Kwadago ta Kano ta aikewa gwamna Abba gida-gida muhimmin sako

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC reshen jihar Kano, ta fito fili ta bayyana cewa za ta goyi bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf a karo na biyu, saboda irin jajircewar da ya ke yi wajen kyautata rayuwar ma’aikata da wadanda suka yi ritaya a jihar.

Shugaban kungiyar kwadago ta NLC na jiha, Kwamared Kabiru Inuwa ne ya bayyana hakan a yayin bikin ranar ma’aikata ta duniya ta shekarar 2025 da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24.

Ya ce Kwamared Inuwa ya yabawa gwamnan bisa kasancewarsa na farko a Najeriya da ya fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi na ₦71,000, yana mai bayyana matakin a matsayin jajircewa wajen rage wa ma’aikata wahalar tsadar rayuwa.

Gwamnatin Kano ta shirya magance matsalar karancin gidaje a jihar – Kwamishinan gidaje

Ya kuma yabawa Gwamna Yusuf bisa yadda yake tabbatar da biyan albashi da fansho akai-akai, da kuma kokarin gwamnatinsa na biyan kudaden fansho na Naira biliyan 16 da ya gada daga gwamnatin da ta gabata.

An kuma yaba da matakin kara mafi karancin kudaden wata-wata da yan Fansho suke karba daga ₦5,000 zuwa 20,000, wanda ya ce hakan ya nuna tausayin gwamnan.

InShot 20250309 102403344

Shugaban NLC ya kuma yabawa gwamnan bisa daukar malamai aiki, da amincewa da karin girma ga ma’aikata, da kuma baiwa ma’aikata horo akai-akai, inda ya bayyana hakan a matsayin wani babban mataki da gwamnatin ta dauka don inganta aikin gwamnati.

“Wadannan nasarorin sun nuna yadda gwamnan ya damu da ma’aikata, don haka muke tabbatar wa Gwamna Yusuf cewa za mu goyi bayansa a zabe mai zuwa,” in ji Kwamared Inuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

“BAMA YI”: Kalma mai alamta tsayuwar alkiyamar raggo ko mutakabirin dansiyasa – Dr. Murtala Iliyasu Ayagi

  Daga Dr. Murtala Iliyasu Ayagi malamin a Kwalejin Koyar...

2027: Tinubu ya bayyana lokacin da zai ambata sunan wanda zai yi masa mataimaki

I'mFadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai...

Ciyaman din Wudil ya kaddamar da aikin gina magudanan ruwa a wasu garuruwa a yankin

Daga Maryam Adamu Mustapha   Shugaban karamar hukumar Wudil, Hon. Abba...