Majalisar Zartaswa ta jihar Kano ta amince da Naira biliyan hamsin da ɗaya da miliyan dari biyar da saba’in da biyar da dubu ɗari bakwai da dari biyar da saba’in da biyar da kobo casa’in da shida (₦51,575,700,575.96) domin aiwatar da wasu muhimman ayyuka da shirye-shiryen da za su inganta rayuwa da walwalar al’ummar jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya sanyawa hannu kuma aka aikowa Kadaura24.

Majalisar ta Amince da kashe kudaden ne a zaman da ta gudanar ranar litinin karkashin jagorancin gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Sanarwar ta ce an ware Naira ₦185,162,487.50 ga Ma’aikatar Kimiyya, Fasaha da Kirkire-Kirkire domin biyan bashin daga 2023 zuwa 2025 da gudanar da wasu aiyuka.
Gwamnatin tarayya ta aiyana ranar hutun ma’aikata
Haka zalika majalisar ta Amince a kashe Naira ₦11,000,000.00 ga Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi domin biyan albashin watanni 11 na masu gadin daji su 100.
An kuma ware Naira ₦327,780,226.89 ga Ma’aikatar Ilimi domin biyan wasu basussuka da su ka jibanci harkar ilimi.
Kazalika majalisar ta Amince a kashe Naira ₦240,506,500.00 ga Ofishin Sakataren Gwamnati domin sayen motocin kashe gobara don amfani a Gidan Gwamnati.
Majalisar ta kuma amince a kashe Naira ₦390,361,730.83 ga Ma’aikatar Ayyuka domin kawowa da saka na’urorin Hawa da mutane bene (elevator) a Gidan Murtala da Gidan Ado Bayero.
Sa’ann za a kashe Naira ₦122,161,145.87 domin gyaran sassan Ma’aikatar KERD.
Haka kuma za a kashe Naira ₦409,444,909.13 domin gudanar da gyare-gyaren masaukin gwamnan jihar Kano da ke kan titin Sultan, Kaduna.
An amince da kashe Naira ₦105,403,453.62 domin aikin hanya daga Miller Road zuwa Mission Road.
Kazalika majalisar ta Amince a kashe Naira ₦1,212,571,013.79 ga Ma’aikatar Ilimi domin inganta Makarantar Karatun Addinin Musulunci (SIS) da ke Dawakin Tofa, Tofa da Ungogo LGAs.
An amince a kashe Naira ₦1,698,800,000.00 ga Ma’aikatar Ruwa domin biyan kuɗin lantarki, dizil da fetur daga watan Janairu zuwa Maris 2025.
Majalisar ta kuma amince da kashe Naira ₦265,803,510.00 ga Ma’aikatar Ƙasa da Tsare-tsare domin biyan diyya ga masu gidajen da aikin fadada jami’ar Aliko Dangote University of Science and Technology, Wudil ya shafa .
Kuma an amince a kashe Naira ₦81,142,850.00 domin biyan diyya ga mutanen da aikin hanyar Panda–Hamdullahi–Albasu–Sakwayen Dutse ya shafa.
Majalisar ta kuma amince da kashe Naira ₦3,469,629,136.81 ga Ma’aikatar Ayyuka domin sanya fitilun kan hanya masu amfani da hasken rana a fadin birnin Kano .
Sauran muhimman abubuwan da aka amince da su sun haɗa da:
Haka zalika majalisar ta Amince a kashe Naira ₦115,959,502.88 domin gyaran masallacin Juma’a a Amana City;
Sa’annan an amince da kashe Naira ₦303,399,484.20 domin gina masallacin Juma’a da wasu ayyuka a Rijiyar Gwangwan, Dawakin Kudu;
Sai kuma Naira ₦274,770,887.84 da aka ware domin gina katanga a Gidan Gwamnati;
Kazalika majalisar ta Amince a kashe Naira ₦1,468,685,912.17 domin gyara da sabunta Ma’aikatar Wuta da Makamashi dake Sharada Phase I;
Majalisar ta kuma amince da kashe Naira ₦5,492,077,139.05 domin gyaran titin da ya tashi daga Gidan Mallam Aminu Kano (Mumbayya House) zuwa Tal’udu Junction, Gadon Kaya, Yahaya Gusau Road har zuwa Sharada .
Sai Naira ₦15,667,634,645.10 da aka ware domin biyan hakkokin sallamar tsofaffin kansiloli da suka yi aiki daga 2014 zuwa 2024;
Haka zalika majalisar ta Amince a Naira ₦5,386,380,955.00 domin ci gaba da shirin bayar da guraben karatu na ƙasashen waje da kuma na cikin gida.