Hajjin bana: Ya kamata gwamnatin tarayya ta dawo da nada Amirul Hajji na kasa – Sarki Sanusi II

Date:

Daga Ummahani Abdullahi Adakawa

 

Mai Martaba Sarkin Kano na 16 Malam Muhammad Sanusi II ne ya bukaci gwamnatin tarayya da ta dawo da nada Amirul Hajji na kasa saboda muhimmancin da hakan ke da shi.

Kadaura24 ta rawaito Sarki Sanusi II ya bayyana hakan yayin da ya karbi tawagar Shugabannin hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Kano a a fadarsa.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Sarkin ya jaddada muhimmancin dawo da nadin Amirul Hajj na kasa, wanda zai rika jagoran tawagar alhazan Najeriya a yayin gudanar da aikin hajji a chan kasa mai tsarki .

Ya kara da cewa nadin Amirul Hajj ya samo asali ne tun a zamanin Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda ya karfafa nadin shugabannin da za su jagoranci al’umma a irin wadannan tafiye-tafiye na ibada.

Hajjin Bana: An sanya ranar da Alhazan Kano za su fara tashi zuwa Saudiyya

Ya kuma jaddada cewa nadin Amirul Hajj na kasa ya zama duba da irin rawar da ya ke tawa a yayin aikin Hajji .

A nasa bangaren, Darakta Janar na Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya ce sun je fadar Sarkin ne domin gayyatar Sarkin domin ya halarci taron aikin Hajji na gwaji da za a gudanar a sansanin Hajji.

InShot 20250309 102403344

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Sulaiman Abdullahi Dederi ya aikowa Kadaura24, ya ce Alhaji Lamin Rabi’u ya kara da cewa Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin fara jigilar Alhazai da aka shirya farawa a ranar 13 ga watan Mayun 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...