Rikici ya barke a cikin jam’iyyar NNPP ta karamar hukumar Dawakin Tofa dake jihar Kano, biyo bayan rushe shugabannin jam’iyyar da shugaban jam’iyyar na jihar, Hashimu Dungurawa ya yi.
Wasu majiyoyi, sun ce matakin na Dungurawa ya gamu da tirjiya daga wasu jiga-jigan jam’iyyar a yankin, wadanda su ka zarge shi da yunkurin dora abokansa kan shugabanci jam’iyyar.

Majiyar KADAURA24 ta Daily Gazzard ta rawaito Shugabannin jam’iyyar da aka rusa sun nuna rashin jin dadinsu da takaicinsu, suna masu ikirarin cewa abun da Dungurawa yayi na rushe su ya sabawa kundin tsarin mulkin jam’iyyar da kuma ka’idojin dimokradiyya.,
An dai zargi Dungurawa da baiwa mutanen da ya nada muhimman mukamai, lamarin da ya haifar da fargaba da rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar.
Da dumi-dumi: Sarki Aminu ya nada sabon Galadiman Kano
Wannan lamari ya haifar da rudani a cikin jam’iyyar musamman idan akai la’akari da yadda zaben shugabannin jam’iyyar ke tafe a nan gaba.
Duk kokarin da aka yi na jin ta bakin Shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Kano Hashim Sulaiman Dungurawa domin ya mayar da martani a kan lamarin da ya ci tura.
Sai dai Shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa, Anas Mukhtar Bello, ya mayar da martani kan zargin da ake yiwa shugaban jam’iyyar NNPP na jihar, Hashimu Dungurawa, inda ya tabbatar da cewa babu wani dan jam’iyyar da zai rasa mukaminsa.
A cewar Anas Bello, abun da aka yi da ake yi a halin yanzu, gyare-gyare ne kawai aka yi da nufin sanya wadanda suka dace cikin kunshin shugabancin daga matakin mazabun karamar hukumar.
Ya kuma bayyana cewa matakin ba shi da alaka da rabon goron Sallah, inda ya yi watsi da hasashen da ake yadawa.