A karon farko Tsangayar Africa Tv3 ta yaye ɗaliban da su ka yi diploma a shari’ar musulunci

Date:

Tsangayar Afirka dake Ƙarƙashin Tashar Talabijin ta Afirka TV3 ta yi Bikin Yaye Daliban da Su ka kammala Karatun Difiluma A kan Shari’ar Musulunci Karon Farko da Tashar ta Ɗauki Nauyin Karatunsu ta INTANETI

Bikn yaye ɗaliban wanda ya kasance shi ne karo na farko da aka gudanar a sabuwar jam’iar Bayero. An shirya ne domin tattara ɗaliban da suka samu damar shiga tsarin koyon karatu na shekarar 2024/2025 .

InShot 20250309 102403344

Da yake jawabi kan dalilan assasa karatun, shugaban gamayyar rukunonin tashoshin Afirka TV3 Dr. Habib Tijjani Taheer, ya ce, “an samar da tsarin ne domin bayar da dama ga masu shawa’ar karatun addinin Musulunci a duniya ta hanya mafi sauƙi, wato ta INTANETI tun a shekarar 2022.
Dr. Habib, ya ce, “hakan zai taimaka wajen sauƙaƙa wa masu shawa’ar karatun a duk inda suke cikin shekara guda.”

Sannan ya ƙara da cewa, ” da farko kusan dalibai dubu goma sha biyar ne suka nemi shiga tsarin karatun, amma a halin yanzu an samu kusan dalibai dubu uku sun kammala karatunsu, da muke fatan zai amfani rayuwarsu da sauran alummar Musulmi baki daya”.

Hajjin Bana: An sanya ranar da Alhazan Kano za su fara tashi zuwa Saudiyya

Haka zalika ” Karatu ne da ya haɗa dalibai ba iya na Nijeriya ba, har ma da sauran ƙasashen duniya. Kuma daga yau za mu fara rijistar sababbin daliban da za su fara karatu a zangon karatu na biyu, sannan za mu duba shawarwarin da aka bayar na samar da tsarin karatun Digiri a nan gaba kaɗan.”

Da yake bayyana tasirin da karatun zai yi ga alumma, ɗaya daga cikin malaman Tsangayar Farfesa Abdulkhadir Isma’il, ya ce, “hakan zai zama wata dama ga dukkan mai son yin karatu a duk inda yake”.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Farfesa Isma’il ya kara da cewa, “ya zama wajibi ga alummar Musulmi su tashi tsaye domin samun Ilimi da a yau talauci ya ke neman kassara shi, ta wannan hanyar da a yanzu duniya take a kansa.”

Da suke bayyana farin cikinsu kan yadda suka amfana da karatun, wasu daga cikin daliban da suka kammala karatun sun godewa Tashar da ta ɗauki nauyin koyar da su.

A ƙarshe an karrama wasu daga cikin waɗanda suka bayar da gudunmawarsu wajen samun nasarar karatun, inda aka ba wa dalibin da ya fi ƙwazo kyautar kujerar Umara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Shari’a ta Kano ta Gargadi Alkalai 2, ta kuma dakatar da Magatakarda 2

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Hukumar kula da shari’a ta jihar...

Amarya Aisha Humaira ta aike da sako ga masu kage kan alakarsu da Rarara

  Aisha Humaira, amaryar kuma abokiyar aikin mawaki Dauda Kahutu...

NUJ ta kaddamar da kungiyar kafafen yada labarai na yanar gizo a Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Kungiyar ‘yan jarida ta kasa NUJ...

Da dumi-dumi: Sarki Aminu ya nada sabon Galadiman Kano

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Mai Martaba Sarkin Kano na 15,...