Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna lokacin da wani ɗan TikTok mai suna Disturbing, wanda ke cikin gungun masu fafutukar ‘JUSTICE FOR MOHBAD’, ya mutu a yayin da ya ke tsaka da watsa bidiyo kai-tsaye.

Wannan labari ya samu tabbaci daga wani dan jarida mai binciken ƙwaƙwat, Temilola Sobola, wanda ya yada wannan bidiyo mai tayar da hankali tare da rubuta: “Wani shahararren ɗan TikTok da aka fi sani da Disturbing, wanda shima yana cikin masu fafutukar JUSTICE FOR MOHBAD, ya rasu wasu awanni da suka wuce a yayin da yake watsa bidiyo kai tsaye…”
LEADERSHIP ta rawaito cewa, Disturbing, wanda ya yi fice saboda jajircewarsa a fafutukar “Justice for Mohbad”, ya bayyana kakar cikin damuwa sosai kafin ya ɓingire, inda daga bisani ya ce ga garin ku nan.