Sare bishiya: Kotu a Kano ta yanke wa wani hukuncin daurin watanni 2 a gidan yari

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Wata kotun majistare da ke zamanta a Rijiyar Zaki a Kano ta yanke wa wani mai suna Alh Inuwa Ayuba hukuncin daurin watanni biyu a gidan yari ko kuma ya biya samakamon samun shi da sare washi bishiyoyin tarbejiya har guda bakwai da ke kauyen Sarauniya a karamar hukumar Dawakin Tofa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na ma’aikatar muhalli ta jihar Kano Isma’il Garba Gwammaja ya aikowa Kadaura24.

IMG 20250415 WA0003
Talla

A cewar Barr. Bahijja H. Aliyu wadda ke jagorantar tawagar ma’aikatan ma’aikatar muhalli sun sami labarin yadda ake sare bishiyoyin darbejiya ba bisa ka’ida ba a kauyen Sarauniya wanda ya saba wa tanadin dokokin ma’aikatar muhalli ta jihar Kano, wanda hakan yasa su kama wanda ake zargin da kuma tare da tattara dukkan hujjojin da suka dace wanda aka gabatar a gaban kotu ta hannun Lauyan masu gabatar da kara Barr Bahijjah H. Aliyu.

Hajjin bana: Saudiyya ta fitar da jerin Harsuna 20 da za a fassara hudubar Arfat da su

Idan za ku iya tunawa Ma’aikatar Muhalli da Sauyin yanayi ta Jihar Kano ta samar da dokokin yaki da gurbacewar muhalli da hana sare bishiyoyin ba tare da samun izini daga hukumomin da abin ya shafa ba .

Lauyan masu gabatar da kara ta ce bayan Kotun ta aminta da hujjojin da aka suka gabatar mata, ta yankewa wanda ake tuhuma hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni biyu sannan kuma an umarce shi da ya dasa bishiyoyin darbejiya 14 a matsayin hukunci kan laifin da ya aikata.

InShot 20250309 102403344

Kwamishinan Muhalli da Sauyin yanayi, Dakta Dahiru M. Hashim, ya yabawa kokarin jami’an tsaro da bangaren shari’a bisa goyon bayan da suke bayarwa wajen kare muhallin jihar.

Ma’aikatar ta bukaci mazauna yankin da su bi ka’idojin muhalli da dokokin gurbacewar muhalli da kuma kai rahoton duk wani abu na lalata muhalli ga hukumomin da suka dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Shari’a ta Kano ta Gargadi Alkalai 2, ta kuma dakatar da Magatakarda 2

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Hukumar kula da shari’a ta jihar...

Amarya Aisha Humaira ta aike da sako ga masu kage kan alakarsu da Rarara

  Aisha Humaira, amaryar kuma abokiyar aikin mawaki Dauda Kahutu...

NUJ ta kaddamar da kungiyar kafafen yada labarai na yanar gizo a Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Kungiyar ‘yan jarida ta kasa NUJ...

Da dumi-dumi: Sarki Aminu ya nada sabon Galadiman Kano

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Mai Martaba Sarkin Kano na 15,...