Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Shahararren mawakin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara zai auri Jarumar Kannywood Aisha Humaira.
Kamar yadda wata majiya ta kusa da Angon ta rawaitowa majiyar kadaura24 ta ta Kano Times wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta ce za a daura auren ne a yau Juma’a bayan sallar juma’a a birnin Maiduguri na jihar Borno.

Majiyar ta bayyana cewa, “An shirya komai, za a daura auren ne a Maiduguri bayan sallar Juma’a.
Rarara ya yi aiki tare da Aisha Humaira tsawon shekaru. Dangantakar su, a cewar majiyar ta wuce ta aiki kadai.
“Rarara ya kan yi wasu daga cikin wakokinsa tare da Aisha, suna da kyakykyawar alaƙa wacce sosai, ga duk wanda ya san dangantakarsu ba zai yi mamakin don ance Rarara zai Auri Aisha Humairah.” in ji majiyar.