Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta fara raba kayan aikin hajjin bana

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Darakta Janar na Hukumar Jin Dadi da Walwalar Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya fara rabon muhimman kayayyakin aikin Hajji ga alhazan jihar da za su tafi kasa mai tsarki.

Alhaji Lamin Rabi’u ya bukaci dukkan masu shirin zuwa aikin Hajji da su yi amfani da kayan da aka raba yadda ya kamata, tare da kaucewa daukar wasu kayayya da hukumar kasar Saudi Arabia ta haramta.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Haka kuma, ya umurci dukkan alhazai da su tuntuɓi jami’an aikin Hajji na kananan hukumominsu domin karɓar kayayyakin.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Sulaiman Abdullahi Dederi ya aikowa Kadaura24.

Yadda gwamnan Kano ya ke rabon kujerun aikin hajjin bana kamar gyada

Bugu da ƙari, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta Najeriya, ta hannun Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON), da ta sake duba batun amfani da katin ATM wajen bayar da kudin alhazai. Ya jaddada bukatar bayar da kuɗaɗen tafiya (BTA) a matsayin kuɗi na hannu domin sauƙaƙa wa alhazai samun damar amfani da su.

InShot 20250309 102403344

A nasa bangaren, Shugaban Majalisar, Daraktoci na hukumar Alhaji Yusif Lawan, ya shawarci alhazan da su yi amfani da kayan da aka raba yadda ya dace.

Kayayyakin da ake rabawa sun haɗa da: jakunkunan hannu, kayan suttura na maza da na mata, hijabai, zobunan hannu , da kananan jakunkuna domin ajiye kuɗi da muhimman takardu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zaizayar kasa: Gwamna Abba gida-gida ya raba diyyar Naira Miliyan 600 A Kano

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Dalilin da ya hana Sarki Aminu Ado Bayero zuwa gidan yari na goron dutse a yau alhamis

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Rahotanni sun tabbatar da cewa Sarkin...

Matakai 3 da gwamnatin Kano ta dauka kan kafafen yada labarai a jihar

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnatin jihar Kano ta ce a...

Yadda manoma a Kano suka zargi jami’an Civil defense da karbar kudade a wajensu

Daga Umar Ibrahim kyarana   Manoman dajin dansoshiya dake karamar hukumar...