Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Kungiyar Samarin Tijjaniya ta kasa tace bata goyon bayan Hukuncin da kotun ECOWAS ta yanke akan batanci ga Janibin Annabi muhammadu SAW.
A wata sanarwa da Kungiyar ta fitar Mai dauke dasa hannun Babban Sakatare Shehu Tasiu Ishaq da sakataren yada labarai Abubakar Balarabe Kofar Naisa Kungiyar tayi tir da Allah wadai da Hukuncin.

Kungiyar tace yin Hukuncin ya sabawa dokokin addinin musulunci, Wanda kuma duk wani Hukuncin da zaici Karo da dokokin Ubangiji bazasu goyi bayansa ba.
Majalisar dokokin Kano da Freedom Radio sun fara musayar kalamai
Daga nan kungiyar Samarin Tijjaniyya ta kasa tayi kira ga Gwamnati a kowane mataki da lallai a tabbatar dabin dokokin da suka tabbatar da tsarin addinin musulunci akan duk Wanda ya keta alfarmar fiyayyen halitta kamar yadda yake a kundin dokokin shari’ar Musulunci.
Kungiyar kuma ta yabawa Gwamnatin Jihar Kano bisa yadda ta jaddada matsayinta na tabbatar da dokokin da suka shafi hukunta duk Wanda yayi batanci ga Janibin Annabi muhammadu SAW Wanda daman tuni dokokin sun kasance na Gwamnatin Jihar ne.
A don hakane ma Kungiyar ta sake jaddada bukatar mabiya dariqar Tijjaniyya da sauran al’umar Musulmi su cigaba da kasancewa masu son zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma bin dokokin addinin musulunci.
Kungiyar Samarin Tijjaniyya ta kasa ta sake bukatar Musulmi su dunga kasancewa masu yin ladabi da biyayya tareda kare duk wata Martaba ta Janibin Annabi muhammadu SAW a kalamansu na yau da kullum.