Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da aikin sake gina babbar hanya daga Abuja zuwa Abuja zuwa Kaduna zuwa Zaria zuwa Kano.
Uba Sani gwamnan Kaduna ne ya wakilci Tinubu a wajen taron.

A wajen taron kaddamar da aikin, wanda ya gudana a Jere a karamar hukumar Kagarko a jiya Lahadi, Sani ya ce titin babbar hanya ce mai matukar muhimmanci ga rayuwar zamantakewa da tattalin arzikin Arewacin Najeriya.
Gwamnatin Kano za ta inganta walwala ma’aikatan dake kula da harkokin kudi – Babbar Akanta
Ya bayyana hanyar a matsayin babbar hanyar da ta haɗa babban birnin tarayya Abuja zuwa sama da jahohi 12 a shiyyar arewa ta tsakiya, arewa maso yamma da arewa maso gabas.
Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa watannin baya Ministan Aiyuka, David Umahi, yayin ƙaddamar da aikin wani sashe na titin ya ce za a kammala aikin titin mai tsawon kilomita 700, ya ce za a kammala shi a cikin watanni 14.