Shuwagabannin jam’iyyar APC da Sakatarorin su na mazabar Kano ta Kudu sun yi kira ga Sanata Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila da ya koma APC.
Da yake jawabi a madadin shugabannin jam’iyyar APC 16 da sakatarorinsu da shugabannin mazabun Kano ta kudu, shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Albasu, Alhaji Iliya Jibrin Hungu, ya ce kiran ya zama wajibi duba da irin kimar da Sanata Kawu Sumaila zai karawa jam’iyyar idan aka koma cikin su.

Hungu ya kara da cewa “idan Sen. Sumaila ya amince da rokonmu ya koma APC, babu wata jam’iyya da za ta haska a Kano ta Kudu, kamar yadda jam’iyyar APC za ta yi .
Da dumi-dumi: Sanata Kawu Sumaila ya kawo aikin sama da Naira Biliyan 120 Kano
“Mun san kwarewa da kimar Sen. Sumaila a siyasar Kano, duk da cewa shi ba dan jam’iyyar APC ba ne, amma duk da haka Kawu yana tallafawa yan duk sauran jam’iyyun ba tare da la’akari da banbancin jam’iyya ba.
“Kawu Sumaila dan siyasa ne da muke bukata a jam’iyyar APC, don haka muna kira ga masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC a Kano ta kudu da shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Barau Jibrin da kuma shugaban jam’iyyar APC na jihar Alhaji Abdullahi Abbas da su taimaka mana wajen ganin Kawu Sumaila ya karbi rokonsu.
Muna da yakinin Sanata Sumaila zai taka rawar gani wajen tallata APC a Kano. Mun yi kewar shi a lokacin da ya bar jam’iyyar, kuma muna kira gare shi da ya dawo ya hada mu don tallata jam’iyyar tare, inji Hungu.
Shugaban ya bayyana cewa jam’iyyar APC na bukatar jajirtattun ‘yan siyasa irin su Sen. Kawu Sumaila wadanda a kodayaushe suke amfani da karfinsu da dukiyarsu domin jin dadin al’ummar mazabarsu.
Nigerian tracker