Rundunar yansanda ta kasa reshen jihar Edo ta tabbatar da kama wasu mafarauta yan asalin jihar Kano dauke da makamai a jihar.
Mafarautan Yusuf Abdulkarim, Mujaheed Garba, Shittu Idris, da Jamilu Habibu an kama su ne a otal ɗin Americanus da ke titin Osemwenkhae, bayan Big Joe Motors, Ramat Park, unguwar Orogbeni, kuma an mika su ga ‘yan sanda.
Daily Trust ta rawaito cewa Rundunar ‘yansandan Jihar Edo ce ta tabbatar da kamen, tana mai cewa an kama su da bindigu.
An rawaito cewa jami’an tsaro na jihar Edo sun kama waɗanda ake zargin a Ramat, unguwar Ikpoba Hill a Benin, dauke da adda da suka boye a cikin jakunkuna.
Babu ja da baya kan dokokin kare kimar addinin musulunci, Gwamnatin Kano ta fadawa kotun ECOWAS
Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar, CSP Moses Yamu, ya bayyana cewa waɗanda aka kama farauta suke yi, ba makiyaya ba kamar yadda aka yada a kafafen sada zumunta.
Ya ce wani mamba na Edo Security Network ne ya cafke su dauke da bindigogi na gargajiya guda uku, harsashi shida marasa cika, harsashi uku da ba su cika ba, adda guda huɗu da wukake biyu.

A cewarsa, ‘yan sanda daga ofishin ‘yan sanda na Ikpoba Hill ne ke gudanar da bincike da tambayoyi a kan waɗanda aka kama.
Hakan ya zo yayin da ake cigaba da alhini da kiraye-kirayen a hukunta waɗanda su ka yi wa mafarauta 16 kisan gilla a garin Uromi na jihar ta Edo.