Kotu a Amurka ta umurci FBI da hukumomin yaƙi da ƙwayoyi su saki bayanan bincike kan Tinubu

Date:

 

Kotun Ƙoli ta Ƙasa ta Washington D.C. a Amurka ta umurci manyan hukumomin tsaron kasar da su fitar da bayanan sirri da suka tattara kan Shugaban Najeriya Bola Tinubu, dangane da wani bincike da ake zargin an gudanar da shi a shekarun 1990.

Premium Times ta rawaito cewa Alƙali Beryl Howell ne ya bayar da wannan umarni a ranar Talata, yana mai cewa hana fitar da irin wannan bayani ga jama’a ba shi da ma’ana kuma ba abin yarda ba ne.

FB IMG 1744283415267
Talla

Wani ɗan ƙasar Amurka, Aaron Greenspan, ne ya shigar da ƙara a watan Yuni 2023 ƙarƙashin dokar ‘Freedom of Information Act’ (FOIA) yana ƙalubalantar ofishin Lauyoyin gwamnatin Amurka, Ma’aikatar Harkokin Waje, FBI, IRS, hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (DEA), da kuma hukumar leƙen asiri ta CIA.

Babu ja da baya kan dokokin kare kimar addinin musulunci, Gwamnatin Kano ta fadawa kotun ECOWAS

A ƙarar da ya shigar, Greenspan ya zargi waɗannan hukumomi da karya dokar FOIA ta hanyar ƙin sakin wasu takardu da suka shafi binciken da ake zargin an gudanar kan Shugaba Tinubu da wani mai suna Abiodun Agbele.

Daga 2022 zuwa 2023, Greenspan ya shigar da buƙatun bayanai 12 zuwa hukumomi shida na Amurka, yana neman bayanai dangane da wani bincike haɗin gwiwa da FBI, IRS, DEA da ofisoshin lauyoyi na gwamnatin tarayya a arewacin Indiana da arewacin Illinois suka gudanar.

InShot 20250309 102403344

Greenspan ya ce takardun da yake nema sun shafi yanke hukunci kan ayyukan da suka haɗa da safarar kuɗi daga haramtattun kwayoyi a birnin Chicago a farkon shekarun 1990s.

A kowanne buƙatun FOIA, ya nemi bayanai kan wasu mutane huɗu da ake zargin suna da alaƙa da wannan ƙungiyar miyagun ƙwayoyi: Bola Ahmed Tinubu, Lee Andrew Edwards, Mueez Abegboyega Akande, da Abiodun Agbele.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yadda gwamnan Kano ya ke rabon kujerun aikin hajjin bana kamar gyada

Daga Rahama Umar Kwaru Al'ummar jihar Kano na cigaba da...

An sulhunta tsakanin Nigeria da Nijar

Gwmanatin Sojin Nijar ta sanar da cewa sun sasanta...

Neman shahara: Hukumar Hisbah ta kama Matashin da ya lashi al’aurar akuya

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Jami’an hukumar Hisbah ta jihar Kano...

2025 Ina Fatan Za ‘ a Yi Aikin Hajjin Da Ba a Taba Yin Irin Sa Ba a Nijeriya – Sheikh Abdullahi Sale Usman

By Ismail Yusuf Makwarari Shugaban hukumar kula da aikin Hajji...