Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta fito da sabbin dabarun aiki da za su saukakawa ma’aikatan ta dake kula da harkokin kudi a ma’aikatu daban-daban wajen aikin su.
Babbar Akanta ta Kano Hajiya Jamila Magaji Abdullahi FCNA ce ta bayyana hakan yayin taron tattaunawa na masu ruwa da tsaki kan fitar da sahihan bayanai da su ka shafi kudi na shekarar 2024 da ta gabata.

Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran ofishin sakataren gwamnatin Kano Alhaji Musa Tanko Muhammad ya fitar.
Babu ja da baya kan dokokin kare kimar addinin musulunci, Gwamnatin Kano ta fadawa kotun ECOWAS
Sanarwar ta kuma ce an shirya taron ne dan sanin yadda za a kara alkintawa tare da kula da harkokin kudade a ma’aikatu.
Da yake jawabi yayin yaron Alhaji Rabiu Abdullahi yabawa gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi kan yadda ya ke samar da abubuwan ci gaba a harkokin tafikar da kudi a nan Kano.