Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Gwamnatin jihar Kano ta yi Allah wadai da hukuncin da kotun ECOWAS ta yanke, inda ta ce wajibi ne a gareta ta kare damar da kundin tsarin mulkin Nigeria ya ba ta na tabbatar da tsare mutuncin addinin mutanen jihar.
Hukuncin kotun ECOWAS, wanda ya bayyana wasu bangarori na dokokin hana yin batanci ga lamuran da suka shafi addinin musulunci a matsayin wadanda suka ci karo da dokokin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa, wanda ya haifar da zazzafar muhawara.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya sanyawa hannu, Hadiminsa Bashir A Bashir ya aikowa Kadaura24.
Ya ce Kano ba zata lamunci karya dokokinta ba, yana mai nuni da cewa doka ce ta baiwa gwamnatin jihar damar yin dokokin da za su tsare addini da al’adun mutanen Kano.
Iya shugabanci: Gwamnan Kano ya sake karbar lambar yabo
Ya ce, “Ba za mu lamunci matsin lamba daga waje ba, alhakinmu ne mu kiyaye addini da al’adun al’ummarmu. Yayin da muke mutunta ra’ayoyin kasa da kasa, dole ne mu tsare mutunta dokokin da suka tsare mutuncin addinin mutanenmu.
“Tsare kimar addinin mutanen jihar da gwamnatin Kano ke yi ya samo asali ne daga kundin tsarin mulkin Najeriya, inda ya baiwa jihohi ‘yancin kafa dokokin da za su kare addini da al’adun al’ummarsu”. Inji Waiya
“Mutanen Kano sun damka mana alhakin wanzar da zaman lafiya da kuma kare martabar addininsu, wadannan dokoki sune jigon wannan aiki, kuma za mu ci gaba da aiki tukuru akan su.”
Yayin da yake amincewa da hukuncin kotun ECOWAS, Waiya ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na kare martabar addini da zaman lafiyar jihar Kano.
Galibin al’ummar jihar Kano dai Musulmai ne , shi ne dalilin da yasa gwamnatin jihar ta yi dokokin da ke hana cin zarafin duk wani abu da ya shafi addinin musulunci.