Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Hukumar kula da kafafen yada labaran na Radio da talabijin ta Kasa NBC ta haramtawa gidajen rediyo da Talabijin na Najeriya sanya wata waka mai suna “Tell Your Papa” wadda fitaccen mawakin nan, Eeedris Abdulkareem ya rera.
Sanarwar da NBC ta fitar ta ce wakar ta yi nuni sosai don haka dole wakar ta zama abar kyama .
A cikin wata sanarwa mai dauke da kwanan watan Afrilu 9, 2025, wadda shugabar hukumar ta NBC Susan Obi, ta fitar, ta bayyana cewa hukumar ta ayyana wakar a matsayin wakar da bata dace a sakata a gidajen radio da talabijin ba saboda ta sabawa sashe na 3.1.8 na dokar yada labarai ta Najeriya.

Wannan sashe ya hana ya duk wasu abubuwan da ake ganin ba su dace ba, kamar zagi, keta mutuncin jama’a a gidajen radio da talabijin a Najeriya.
Damina: Gwamnati ta bayyana jihohin da za su iya fuskantar ambaliyar ruwa a Nigeria
A cewar NBC, waƙar ta sami karbuwa a dandalin sada zumunta, abubuwan da ke cikin waƙar ta sun karya ka’idojin hukumar .
NBC ta haramta sanya wakar Eedris Abdulkareem mai suna “Tell your Papa” don haka ta gargadi duk kafafen yada labarai na radio da talabijin a fadin Nigeria da su guji yada wakar.
A cikin waƙar dai Mawakin ya soke shugaban kasa Tinubu ta hanyar aika sako ga Shugaban kasar ta hannun dansa Seyi Tinubu.