Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za a fuskanci mamakon ruwan sama da zai haddasa ambaliyar ruwa a jihohi 30 da kuma Abuja babban birnin tarayyar kasar a daminar bana ta 2025.
Ministan albarkatun ruwa, Joseph Utsev, ne bayyana haka a ranar Alhamis a yayin gabatar da hasashen kan ambaliyar ruwa wanda hukumar da ke kula da rafuka ta kasar NIHSA ta yi.

Jihohin da za su iya fuskantar ambaliyar ruwan sun hadar da Legas da Ogun da Abia da Ondo da Adamawa da Akwa Ibom da Anambra da Bauchi da Benue da Borno da Bayelsa da Cross-River.
Sauran su ne Delta da Ebonyi da Edo da Gombe da Imo da Jigawa da Kebbi da Kogi da Kwara da Nasarawa da Neja da Osun da Oyo da Rivers da Sokoto da Taraba da Yobe da Zamfara da kuma birnin tarayya Abuja.
Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria
Ministan ya ce wasu bangarori na yankin kudu maso kudancin kasar za su fuskanci ambaliya ta gabar tafkuna da rafuka.
Jihohin sun hadar da Bayelsa da Cross-River da Delta da Rivers, yayin da Akwai-Ibom da kuma Edo za su kasance cikin mummunan hadarin ambaliyar ruwa.
A cewar ministan, ambaliyar ruwa ita ce babbar masifar yanayin da ke daidaita mutane da albarkatun kasa a Najeriya sannan kuma sauyin yanayi ne ke kara hadarin afkuwa ambaliyar.
Joseph Utsev, ya ce jihohin da suka hadar da Abia da Benue da Legas da Bayelsa da Rivers da kuma na daga cikin jihohin da ke cikin hadarin fuskantar ambaliyar ruwa.