Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa
Sabon Shugaban hukumar raya kogunan Hadeja-Jama’are Engr. Rabi’u Sulaiman Bichi da sauran abokan aikina su biyar sun shiga ofis domin kama aiki a matsayin Shugabannin hukumar.
Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito watanni kusan hudu da suka gabata Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya nada Rabi’u Sulaiman Bichi a matsayin shugaban hukumar raya kogunan Hadeja-Jama’are da kuma Musa Iliyasu Kwankwaso a matsayin babban daraktan kudi da harkokin mulki na hukumar da karin wasu mutane 3.
A ranar talata ne sabbin Shugabannin suka kama aiki bayan da Masoya da magoya bayansu suka yi musu rakiya domin shaida yadda za su kama aikin.
Da yake jawabin shugaban hukumar Engr. Rabi’u Sulaiman Bichi ya yiwa al’ummar Jihohin Kano Jigawa da Bauchi albishirin inganta harkokin noma da samar da aiyukan yi ga matasa masu tarin yawa.
” Wannan ma’aikatar babbar ma’aikata ce da za mu yi amfani da ita wajen tallafawa yan jam’iyyar APC, don haka nake sanar da cewa ba sai kun wahalar da kanku wajen zuwa Wannan hukuma ba za mu tsare-tsaren da tallafin mu zai iske ku duk inda kuke”. Inji Engr. Rabi’u Sulaiman
Gwamnatin Nigeria za ta ci gaba da sayar da ɗanyen mai a farashin Naira
Shi ma a nasa jawabin Babban Daraktan Kudi da Mulki na hukumar raya kogunan Hadeja-Jama’are Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi alkawarin duk duk mai yiwuwa don inganta rayuwar al’ummar Jihohin Kano Jigawa da Bauchi.
” Muna godewa dukkanin masoya da magoya bayanmu da suka rako mu wannan ma’aikatar kuma muna baku tabbacin za ku dara sosai, don haka a cigaba da yi mana Addu’ar Allah ya ba mu ikon sauke nauyin da Shugaban kasa ya dora mana”. Inji Musa Iliyasu
Musa Iliyasu Kwankwaso ya kuma godewa shugaban kasa Bola Tinubu da Shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje bisa yadda suka ba su Wannan dama don hidimtawa al’ummar Jihohin Kano Jigawa da Bauchi.