Sanata Kawu Sumaila ya Raba Babura 150 ga wasu yan Kano ta Kudu

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Sanata Suleiman Abdurrahman Kawu Sumaila, ya raba babura 150 a fadin kananan hukumomi 16 dake amazabar sanatan Kano ta Kudu a wani yukuri na tallafawa wadanda suka taimakawa tafiyar gidan Siyasarsa.

Tallafin ya shafi mutane da dama, da suka hada da magoya bayansa guda uku-uku na kananan hukumomi 16, da mabiya addinin Musulunci dana Kirista, da kungiyar Waraka Media, da Waraka Band, jami’an tsaro na Waraka, da sauran mabiya da dama daga sassan jihar Kano.

InShot 20250309 102403344
Talla

Da yake jawabi yayin bikin rabon tallafin, Sanata Kawu Sumaila, ya bayyana cewa ya samar da baburan ne domin tallafawa wadanda suka yi dawainiya da takararsa har ya sami nasara.

“Rabon wadannan babura kari ne kan godiya bisa yadda kuka jajirce akan takarar Kawu Sumaila har ya sami don haka na ga dacewar kuma na gode muku ko kwa kara kwarin gwiwa”.

Rundunar Yansanda ta gayyaci Sarki Sanusi II

A wata sanarwa da mai taimakawa sanatan kan harkokin yada labarai Abbas Adam Abbas ya fitar, ya ce Kawu ya kuma yi alkawarin cigaba da tallafawa wadanda suka dafa masa tare kuma da gudanar da aiyukan da kowanne dan Kano ta Kudu zai amfana.

Wannan dai shi ne karo na shida da Sanata Kawu Sumaila ke tallafawa mutanensa tun bayan hawansa mulki a ranar 13 ga watan Yunin 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Sanata Kawu Sumaila ya kawo aikin sama da Naira Biliyan 120 Kano

Daga Isa Ahmad Getso   Sanatan Kano ta kudu Sulaiman Abdulrahman...

Inganta ilimi: Gwamnan Kano ya zama Gwarzon Shekarar 2024

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Yanzu-yanzu: Sarki Sanusi ya nada sabon Galadiman Kano

Daga Sani Idris maiwaya   Mai Martaba Sarkin Kano na 16...

Babu wata baraka a hukumar NAHCON – Farfesa Abdullah Pakistan

Shugaban Hukumar kula da aikin hajji A ta Najeriya...