Rundunar Yansanda ta gayyaci Sarki Sanusi II

Date:

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gayyaci Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, domin amsa tambayoyi kan wani lamari da ya faru a yayin bikin Sallah karama a Kano.

Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta ruwaito cewa a ranar Lahadi, 30 ga Maris, 2025, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani Usman Sagiru, mai shekaru 20, dan unguwar Sharifai, bisa zargin kisan wani dan Vigillante dake cikin tawagar Sarki Sanusi II bayan sallar idi.

Hakazalika rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin wanda hakan ya sa ya gayyaci Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku domin ya amsa wasu masa tambayoyi.

InShot 20250309 102403344
Talla

 

A cewar wata wasika a hukumance da Kadaura24 ta gani mai dauke da kwanan watan Afrilu 4, 2025, kuma mai dauke da sa hannun CP Olajide Rufus Ibitoye, kwamishinan ‘yan sanda (Ayyuka), an gayyaci sarki Sanusi ne bisa umarnin babban sufeton ‘yan sandan Nigeria.

Wasikar ta bukaci Sarkin da ya kai kansa hedikwatar rundunar da ke Abuja sashin tattara bayanan sirri a ranar Talata, 8 ga Afrilu, 2025, da karfe 10:00 na safe.

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da ranakun komawa makaranta

Hukumomin tsaro sun bayyana hana hawan sallah, saboda yiwuwar samun tashin hankali.

An dai zargi Sarki Muhammadu Sanusi da yin hawa ranar Sallah da hawan daushe da kuma Hawan Nasarawa inda ya kai ziyara ga gwamnan jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...