Rasuwar Galadima: Gwamnan Kano ya mika ta’aziyyarsa ga Sarki Sanusi da shugaban APC Abdullahi Abbas

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Gwamnatin jihar Kano ta mika sakon ta’aziyya ga mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, Majalisar Masarautar Kano da kuma Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alh. Abdullahi Abbas da sauran iyalai, bisa rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi.

Marigayi Galadiman Kano, wanda ya rasu yana da shekaru 91 a daren ranar Talata a Kano, ya kasance fitaccen dattijo kuma jigo a masarautar Kano. Ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa Masarautar, ya rike manyan mukaman sarauta da suka hada da Wamban Kano, ya kuma taka muhimmiyar rawa a Masarautar a karkashin marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.

InShot 20250309 102403344
Talla

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana wannan rashin a matsayin babban rashin, ba wai ga Masarautar kadai ba har ma da jihar da daukacin al’ummar Kano baki daya

Murtala Garo ya mika ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi

Gwamna Abba Kabiru ya yaba da kyawawan halaye na Marigayi Galadiman Kano, a matsayinsa na mutum mai kishi da jajircewa wajen kiyaye al’adun Kano.

Bugu da kari, gwamnan ya jajantawa daukacin al’ummar jihar Kano, bisa babban rashi na Alhaji Abbas Sanusi. Ya kuma yi addu’ar Allah ya jikansa da rahama ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure wannan babban rashi.

Gwamna Yusuf ya bukaci al’ummar Kano da su rika sanya marigayi Galadiman Kano a cikin addu’o’insu don neman masakuma kiyaye kimar hadin kai da hidima da ya tsaya a kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...