Murtala Garo ya mika ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi

Date:

Daga Maryam Adamu Mustapha

 

Tsohon mataimakin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Kano, Hon. Murtala Sule Garo, mika sakon ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano kuma babban dan majalisar masarautar Kano, Alhaji Abbas Sunusi Bayero, wanda ya rasu yana da shekaru 92 .

A wata sanarwa da ya sanyawa hannu da kansa ranar Laraba, Garo ya bayyana marigayi Galadiman Kano a matsayin wani dattijo mai daraja wanda ya bayar da gudunmawa sosai wajen ci gaban Kano da kuma sha’anin sarauta a arewacin .

InShot 20250309 102403344
Talla

“Rasuwar Alhaji Abbas Sunusi babban rashi ne, ba ga iyalansa kadai ba, har ma ga daukacin Masarautar Kano da kuma al’ummar jihar baki daya, domin mutum ne mai hikima da rikon amana, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa al’umma.” Inji Garo.

Murtala Sule Garo, wanda tsohon kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar Kano ya yi addu’ar Allah ya jikan marigayin, ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure wannan babban rashin.

Hotunan yadda aka yi Jana’izar Galadiman Kano

“Ina mika ta’aziyyata ga Abdullahi Abbas shugaban jam’iyyar APC na Kano da daukacin iyalan Galadima, Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma ba shi Aljanatul Firdaus,” Inji Garo

Idan za a tunawa Kadaura24 ta rawaito Allah ya yi wa Alhaji Abbas Sunusi rasuwa a daren ranar Talata, inda ya bar ‘ya’ya da jikoki da dama.

An haife shi a shekarar 1933 a garin Bichi na jihar Kano, ya taba zama Wamban Kano kafin Sarki Sanusi Lamido Sanusi ya nada shi sarautar Galadiman Kano a shekarar 2014.

Galadiman Kano ya ba da gudunmawa sosai wajen cigaban harkokin Masarauta da abubuwan da suka shafi shugabanci a Kano.

Tuni dai aka gudanar da jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, inda manyan mutane daga sassa daban-daban na jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Masu son yi wa Sanata Natasha kiranye ba su cika sharudda ba – INEC

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana cewa buƙatar...

Gwamnan Kano ya yi alwashin kawo karshen matsalar ruwa a masarautar Rano

  Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi alwashin...

A A Zaura ya mika ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi

Tsohon dan takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam'iyyar...

Hawan Sallah: Ƴansanda sun sake gayyatar Hadimin Sarki Sanusi kan zargin bijirewa umarni

  Rundunar ƴansandan jihar Kano ta gayyaci Shamakin Kano, Alhaji...