Rundunar ƴansandan jihar Kano ta gayyaci Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku domin amsa tambayoyi kan zargin saɓa wa umarnin da ƴansandan su ka bayar na haramta Hawan Sallah a Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanyawa hannu kuma aka aikowa Kadaura24.
Ya ce rundunar ta jaddada matsayinta na haramta Hawan Salla a faɗin jihar, kuma duk wanda aka samu da laifin saɓa umarnin zai ɗanɗana kuɗarsa.

Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito a ranar Juma’ar da ta gabata ne dai rundunar ƴansandan jihar ta fitar da sanarwar haramta Hawan Sallah a Kano bayan da ta ce ta samu bayanan sirri na wasu ɓata-gari da ke da aniyar haifar da tashin hankali a lokacin hawan.
Hotunan yadda aka yi Jana’izar Galadiman Kano
Haka kuma sanarwar ta ce kwamishinan ƴansandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori ya kafa wani kwamitin ƴansanda mai mambobi takwas domin gudanar da bincike kan tashin hankalin da aka samu a ranar Sallah lokacin da tawagar Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi ke komawa gida bayan jagorantar Sallar Idi.
A lokacin da aka samu hatsaniyar dai an kashe wani jami’in sintiri tare da raunata wani da ke aikin bayar da tsaro ga tawagar sarkin na 16.