Ɗan majalisar Sarki mafi daɗewa a masarautar Kano, Abbas Sanusi, ya rasu ya na da shekaru 92.
Marigayin wanda dan marigayin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ne, shi ne Galadiman Kano, muƙami mafi girma a majalisar Sarki, ya rasu ne a jiya Talata, 1 ga Afrilu, a Kano, bayan ya sha fama da jinya.

Abbas Sanusi, wanda ya taba zama dan Majalisar Masarautar Kano kafin samun ‘yancin kai, mahaifinsa, Sarki Sanusi na daya ya nada shi a matsayin Sarkin Dawakin Tsakar Gida da Hakimin Ungogo a 1959.
Ya zama Dan Iyan Kano a 1962 a zamanin Sarki Muhammadu Inuwa, sannan kuma a zamanin Sarki Ado Bayero ya zama Wamban Kano.
Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa Galadiman Kano Rasuwa
Ya samu matsayi mafi girma na Galadiman Kano a zamanin mulkin dan uwansa Sarki Muhammadu Sanusi II.

An haife shi a 1933 a garin Bichi, inda marigayin ya fara karatunsa a makarantar Elementary ta Kofar Kudu a 1944 kuma ya halarci makarantar Midil ta Kano (Kwalejin Rumfa a yau) a 1948.
Daga cikin ‘ya’yansa akwai Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na yanzu.
Za’ayi Sallar Jana’izarsa a Kofar Kudu, da misalin karfe 10 na safiyar nan.