Abubuwan da ya kamata ku sani game da Galadiman Kano Abbas Sanusi

Date:

 

Ɗan majalisar Sarki mafi daΙ—ewa a masarautar Kano, Abbas Sanusi, ya rasu ya na da shekaru 92.

Marigayin wanda dan marigayin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ne, shi ne Galadiman Kano, muΖ™ami mafi girma a majalisar Sarki, ya rasu ne a jiya Talata, 1 ga Afrilu, a Kano, bayan ya sha fama da jinya.

IMG 20250330 WA0005
Sakon Barka da Sallah

Abbas Sanusi, wanda ya taba zama dan Majalisar Masarautar Kano kafin samun β€˜yancin kai, mahaifinsa, Sarki Sanusi na daya ya nada shi a matsayin Sarkin Dawakin Tsakar Gida da Hakimin Ungogo a 1959.

Ya zama Dan Iyan Kano a 1962 a zamanin Sarki Muhammadu Inuwa, sannan kuma a zamanin Sarki Ado Bayero ya zama Wamban Kano.

Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa Galadiman Kano Rasuwa

Ya samu matsayi mafi girma na Galadiman Kano a zamanin mulkin dan uwansa Sarki Muhammadu Sanusi II.

InShot 20250309 102403344
Talla

An haife shi a 1933 a garin Bichi, inda marigayin ya fara karatunsa a makarantar Elementary ta Kofar Kudu a 1944 kuma ya halarci makarantar Midil ta Kano (Kwalejin Rumfa a yau) a 1948.

Daga cikin β€˜ya’yansa akwai Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na yanzu.

Za’ayi Sallar Jana’izarsa a Kofar Kudu, da misalin karfe 10 na safiyar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related