Allah ya yi wa Galadiman Kano Alhaji Abbas Sunusi rasuwa.
Wata sanarwa da ta fito daga guda daga cikin iyalan sa ta shaidawa DWHausa cewar nan gaba za’a bayyana lokacin Jana’izar sa.

Alhaji Abbas Sunusi, Kawu ne ga Sarkin Kano na 16 Muhamamd Sunusi na biyu, kuma mahaifi ga shugaban Jamiyyar APC na jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas.
Marigayin shi ne Wamban Kano babban Dan majalisar Sarki kafin daga bisani aka daga likkafar sarautar sa zuwa Galadiman Kano.