Kisan Gilla: Gwamnatin Kano ta yabawa Tinubu da gwamnan Edo

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Gwamnatin Jihar Kano ta gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, saboda gaggawar ɗaukar matakin da su ka yi bayan kisan gillar mutane 16 ’yan asalin Kano a Udene, da ke ƙaramar hukumar Uromi ta Jihar Edo.

Gwamnan ya sake buƙatar a gudanar da shari’a ta gaskiya, tare da bayyana waɗanda aka kama a fili, domin tabbatar da cewa an yi adalci.

Gwamna Abba Kabir Yusuf, a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa-hannun Kwamishinan yaɗa labarai, Kwamared Ibrahim Waiya, ya yaba wa tawagar Gwamnatin Tarayya da Gwamnan Edo saboda ta’aziyyar da ya zo Kano, da kuma kudurin su na tabbatar da adalci ga waɗanda aka kashe.

IMG 20250330 WA0005
Sakon Barka da Sallah

Ya kuma yaba wa Gwamnan Edo saboda tattaunawa da al’ummar Hausawa a Jihar Edo da kuma alƙawarin biyan diyya ga iyalan waɗanda suka rasu.

Haka kuma Gwamnan ya yaba Shugaba Tinubu bisa umarnin da ya bai wa hukumomin tsaro domin gano waɗanda ke da hannu a kisan, wanda ya bayyana hakan a matsayin ƙwazon da Gwamnatin Tarayya ta nuna wajen kare dukkan ’yan Najeriya.

InShot 20250309 102403344
Talla

Gwamnatin Jihar Kano ta kuma yi alƙawarin ci gaba da sa ido kan lamarin don tabbatar da adalci da biyan diyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...