Daga Kamal Yakubu Ali
Akalla kimanin mabukata maza da mata 500 ne su ka amfana da zakkar Naira dubu Ashirin- ashirin Wanda hukumar zakkah da hubusi ta jihar Kano ta gudanar a yau Litinin da aka gudanar farfajiyar hukumar dake kan titin airport road.
Da yake jawabi ga ‘yan jarida shugaban hukumar zakkah da hubisi ta Jihar Kano Barista Habibu Dan almajiri Fagge ya ce wannan zakkah wasu manyan attajirai ne a jihar kano su ka fidda zakkar su su ka kuma mikawa hukumar zakkah da hubisi ta Jihar Kano don su rabawa mabukata.

Cikin wadanda suka Bayar da zakkar sun hadar da attajirin Dan kasuwar nan Alhaji Aminu Alhasan Dantata Wanda ya ba da( naira miliyan biyar)5000000 sai Kuma Alh.Mustapha Amasco Wanda shi ma ya ba da (naira miliyan biyar) 5000000 sai Kuma wani bawan Allah Wanda ya ba da dubu dari biyar, dukkaninsu domin a tallafawa mabuka, kamar yadda shugaban hukumar zakkah da hubisi ta Jihar Kano Barista Habibu Dan almajiri Fagge ya bayyana .
Sarki Aminu Ado Bayero ya fara daukar matakan gudanar da Hawan Sallah Karama a Kano
Shi ma a nasa Jawabin kwamashi na Daya a hukumar M.Nafi’u Umar Harazumi kira yayi ga mawada su cigaba da tallafawa hukumar wajen ba da zakkarsu ga hukumar domin rabawa ga mabukata .
Wasu daga cikin wadanda suka amfana da zakkar sun yabawa hukumar sannan suka godewa wadanda suka ba da zakkar.
Wakilinmu ya bamu labarin cewa taron ya samu halartar al’umma dama .