Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Tsohon ɗan takarar majalisar tarayya a zaɓen 2019, Kwamared Adnan Mukhtar Tudun-Wada, ya yi kira ga Seyi Tinubu da ya daina rangadin buɗa-baki a yankin Arewa, yana mai cewa hakan cin mutunci ne ga al’ummar yankin.
A wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Talata a Abuja, Adnan, wanda kuma shi malami ne a jami’a kuma kwararren jami’in hulɗa da jama’a ne, ya bayyana cewa rabon shinkafa da ɗan shugaban ƙasa ke yi a cikin kwanakin nan yana rage kimar Arewa.
Ina so in gaya wa ɗan Shugaban Kasa cewa wannan ba lokacin yaƙin neman zaɓe ba ne. Shekara biyu kenan zuwa 2027. Idan yana son taimakawa Arewa, ya fi dacewa ya kawo hanyoyin da za su inganta rayuwar matasa, ba sai da kayan tallafi ba,” inji Adnan.

Ya kuma caccaki gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu bisa yadda ta ke tafiyar da harkokin ƙasa, yana mai cewa Arewa na fuskantar matsaloli masu yawa da suka hada da rashin tsaro, durƙusar masana’antu, da gazawar kammala hanyoyin da suka haɗa yankin da sauran sassan ƙasa.
“A bar Shugaban Kasa ya mayar da hankali kan matsalolin Arewa. Amma zuwan ɗansa yana raba mana abinci, tamkar mabarata, abin kunya ne,” inji shi.
Cin zarafi: Gwamnatin Kano za ta sanya kafar wando da sojojin baka – Kwamared Waiya
Ya kuma soki yadda Seyi Tinubu ke halartar fadar sarakunan gargajiya a Arewa ba tare da mutunta al’adun yankin ba. “Shin zai iya yin hakan a Kudu? Zai iya shiga fada ya zauna haka a gaban Oba na Legas ko Oni na Ife?”.
Daga ƙarshe, Adnan ya yi kira ga matasan Arewa da su guji goyon bayan abubuwan da Seyi Tinubu ke yi, yana mai cewa ba shi da wani mukamin siyasa kuma ba shi da hurumin yin irin waɗannan ayyukan.