Hatsari Guda Biyu da Su ka Canza Rayuwar Matashi Nuraddin, Amma ba su Dakushe Burinsa ba

Date:

Nuraddin ya fuskanci manyan jarabawa guda biyu a rayuwar sa—hatsarurruka da suka bar shi da nakasa, amma bai bar hakan ya hana shi ci gaba da rayuwa da kwazon sa ba.

An haifi Nuraddin a shekarar 1991 a karamar hukumar Gwarzo, jihar Kano. Rayuwar sa ta fara kamar ta kowane yaro mai lafiya, ya kuma fara makarantar firamare da himma. Bayan kammala firamare a 2003, ya shiga sana’ar injin nika don tallafawa iyayensa. A nan ne hatsari na farko ya auku—hannunsa ya makale a injin nika, wanda ya tilasta a yanke shi. Duk da haka, bai karaya ba, ya koma sana’ar sayar da fetur a bakin titi, har ya samu damar ci gaba da karatun sakandire.

Bayan ya kammala sakandire a 2014, ya samu gurbin karatu a Northwest University, Kano, kuma ya dauki nauyin kansa har ya kai ga bautar kasa a 2019. Lokacin da ya shiga sansanin NYSC, an ba shi damar komawa gida saboda lalurar da ke tare da shi, amma ya nace cewa zai iya yi wa kasa hidima a ko’ina.

InShot 20250309 102403344
Talla

Hakan ya kai shi Taraba, inda hatsari na biyu ya faru. A hanyarsu ta zuwa garin Gembu, motarsu ta yi mummunan hadari. A sakamakon haka, hannunsa na dama ya yanke, kuma idonsa guda daya ya samu matsala mai tsanani. An dauki tsawon lokaci ana jinyar sa, an kuma yi masa aiki don sanya hannun roba. Duk da matsalolin da suka faru, bai tsaya ba—ya cigaba da kokarin inganta rayuwarsa.

A karshe, Nuraddin ya samu aiki a Kano State Polytechnic, daga nan kuma aka tura shi Nigeria Social Insurance Trust Fund (NSITF). Duk da irin jarabawarsa, bai taba barin burinsa ba.

Zargin Handama: Al’ummar Garin Danzaki Sun Nemi Agajin Gwamnan Kano

Yanzu haka yana fuskantar wasu kalubale biyu: jinkirin ci gaba da kula da idonsa a Kaduna, da kuma sharadin da asibitin Legas ya gindaya na komawa bayan wata uku don duba hannun roba da aka sanya masa.

Nuraddin ya zama abin koyi na jajircewa, kwazo, da nuna cewa nakasa ba ita ce karshen rayuwa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Majalisar Wakilan Nigeria ta bayyana Matsayarta Kan dokar ta baci a jihar Rivers

  Majalisar wakilan Nigeria ta Amince da dokar ta baci...

Cin zarafi: Gwamnatin Kano za ta sanya kafar wando da sojojin baka – Kwamared Waiya

Daga Isa Ahmad Getso   Gwamnatin jihar Kano ta ce ta...

Gobarar Kwalema: Atiku Abubakar ya jajantawa Matawallen Gwagwarwa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku...

Gwamnan Kano ya nada mataimakin mai magana da yawunsa da wasu mukamai

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince...