Daga Rahama Umar Kwaru
Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC reshen jihar Kano sun kama shahararriyar yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya bisa zargin cin zarafi Naira.
Kadaura24 ta rawaito hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa hukumar EFCC ta fitar a sashin shafinta na Facebook.
EFCC ta ce ta kama Murja Kunya ne bisa zarginta da laifin dikin takardar kudin Naira haka kawai don jin dadi a wani lokacin da take zaune a dakin otal di Tahir Guest Palace a Kano.

An kamata ne bayan da ta gudu bayan da hukumar ta EFCC ta ba da Belinta tsawon wata daya da ya wuce, wanda hakan yasa jami’an hukumar suka fara farautarta.
Tun da farko an kama ta ne a watan Janairun 2025 da zargin laifin karya dokokin babban bankin Najeriya CBN, dokar da ta haramta cin zarafi da lalata Naira.
Sai dai kuma bayan kwashe tsawon makonni ana bincike da kuma sa ido, jami’an EFCC sun yi nasarar sake kama Murja kunya a ranar Lahadi 16 ga Maris, 2025. Daga nan kuma aka mika ta zuwa Hukumar Shiyya ta Kano, inda a halin yanzu take tsare tana jiran a gurfanar da ita a gaban kuliya.
Ɗan Gwamnan Bauchi ya caccaki Dan Shugaban kasa Seyi Tinubu
Hukumar ta EFCC ta sake jaddada kudirinta na aiwatar da dokokin da ke kare mutuncin kudin Najeriya sannan ta yi gargadi kan ayyukan cin zarafi da suka hada da yin likin kudi ko wulakantar da Naira a lokutan bukukuwa.