Shamsuddeen Bala Mohammed, dan gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya yi kira ga Seyi dan shugaban kasa Bola Tinubu da kada ya maida matasan jihar almajirai idan ya zo jihar a ziyarce-ziyarce da ya ke yi zuwa jihohi.
PUNCH ta rawaito cewa, Mohammed, a wani sako da ya wallafa a Facebook a jiya Lahadi, ya bukaci Seyi da ya samarwa matasan Bauchi guraben ayyukan yi, da jari su fara kasuwanci, da horar da su kan kasuwanci na crypto, da sauran nau’o’in karfafawa maimakon raba musu abinci a roba.

Ya ce, “ Lokacin da za a zo Bauchi, a ba wa matasan mu aikin yi, a basu Keke NAPEP, kuɗaɗe don fara kasuwanci, a karfafa su akan fasahar zamani, Wato ICT da horar da su kan kasuwancin crypto da sauransu.
“Don Allah, mu matasan Bauchi ba mu bukatar shinkafa da abinci a leda a cikin watan Ramadan. A koya wa matasanmu yadda ake kama kifi, maimakon ciyar da su na kwana guda.
“Ba almajirai ba ne.”
Iftila’i: An sanya dokar hana fita a Jigawa
Ya jaddada cewa matasan Bauchi ba sa bukatar tallafin abinci sai dai dama don dogaro da kai.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa an hangi Seyi Tinubu yana raba abinci ga mabukata a ziyarar da ya kai wasu jihohin Arewa.