Daga Ibrahim Sani Gama
Kungiyar cigaban matasan unguwar Rimin Kebe karshen Kwalta dake karamar hukumar Ungogo ta Koka da yadda wasu matasa a yankin su ke hada-hadar muggwan kwayoyi da tabar wiwi da zama a wani fili dake Unguwar, wanda hakan yana kawo barazana ga lafiya da dukiyoyin al’umma yankunan.
Danlami Kabiru da Abdulrahaman Bello ne su ka yi koken a madadin al’ummar yankin ga jaridar Kadaura24 .
Danlami Kabiru ya bayyana cewar, hada-hadar Muggwan Kwayoyi ya zama Ruwan dare duk da cewa yanzu lokacin watan Azimi ne, Amma Matasan basa daga kafa wajen Shaye Shaye da Kasuwancin Muggwan Kwayoyi.

Ya ce, dangane da haka Kungiyar Matasan yankin take sanar da gwamnati da sauran mahukunta da masu ruwa da tsaki da hukumar hana Sha da Fataucin miyagun Kwayoyi da su shigo domin tallafawa al’ummar wannan yanki duba da halin suka samu kansu a ciki.
Danlami Kabiru ya kara da cewar,. a kwanakin baya Kungiyar ta gudanar da taro da masu zama a filin da suke shaye Shayen tare yin kira a gare su da su dakatar da zaman da su ke yi a wannan wuri, Inda suka dauki alkawarin ba za su kara zama a filin ba, Amma daga bisani suka dawo tare da ci gaba harkokinsu na hada-hadar muggwan Kwayoyi.
Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu
A jawabinsa Abdulrahaman Bello, ya kira al’ummar yankunan na Rimin Kebe karshen kwalta da masu Ruwa da tsaki da masu Hannu da Shuni da taimaka wajen yakar wannan Mummunar Dabi’ar da Wasu daga cikin matasan Unguwar Rimin Kebe karshen Kwalta Suke a wannan Fili.
Bugu da kari kungiyar matasan unguwar Rimin Kebe Karshen Kwalta,ta Kuma bukaci mamallakin Filin da ake yin Shaye Shayen dake layin Sule Dankano da ya zo ya gina shi domin a samu damar dakatar da Abubuwan da ake yi a Filin Wanda yanzu haka mata ma Sun fara daukar wannan Dabi’a.
Daga Karshe Kungiyar ci gaban Unguwar Rimin Kebe Karshen Kwalta, ta Yi Kira Maiunguwa Malam Miko da ya taimakawa Kungiyoyin Yankunan domin tallafawa na kawo Karshen Kasuwancin Muggwan Kwayoyi da Tabar wiwi da zama Shaye Shaye a Unguwar Rimin Kebe Karshen Kwalta.