Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Date:

Daga Kamal Yakubu Ali

 

Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad Umar ya bukaci hukumar zakka da hubusi ta jihar Kano da ta kara fadada ayyukanta izuwa kananan hukumomi 44 da muke da su ta yadda za’a tallafawa mabukata duba da halin matsi da kunci da ake ciki.

Mai Martaba Sarkin Rano ya bayyana hakan a yayin da ya karbi bakuncin ayarin shugabannin Hukumar Zakka da Hubusi ta jihar Kano a Fadar sa dake Garin Rano.

InShot 20250309 102403344
Talla

Mai martaba ya ce inganta ayyukan hukumar zakka da Hubusi wata hanyace da gwamnati za ta bi domin tallafawa al’umma ta hanyar rage musu talauci da fatara .

Ya kuma bayyana cewa zakka wani Rukuni ne daga rukunan addinin Musulunci dan haka dole ne a bata kulawar da ta dace.

Shaye-shayen kwayoyi: Al’ummar Unguwar Rimin Kebe sun nemi agajin mahukunta

Dr Muhammad umar yasha alwashin yin duk mai yiwuwa don baiwa hukumar zakkar dukkanin wasu shawarwari da hadin kai da kuma goyon baya domin inganta aiyukansu.

Da yake Jawabinsa tunda farko ,Shugaban Hukumar Barista Habibu Dan Almajir ya ce sun kai ziyara fadar Sarkin ne don neman cikakken goyan bayan Masarautar ta Rano domin inganta ayyukan hukumar kasancewar sarakuna sune iyayen kasa kuma sune sukafi kusanci da alumma.

Shugaban Hukumar Barista Habibu Muhammad Dan Almajir ya Kuma yabawa Masarautar Rano bisa irin Tarbar da akayi Musu.

Barrister. Dan Almajiri sun ziyarci fadar ne tare da Rakiyar shugabannin hukumar da suka hadarda Commissioner l Malam Nafi’u! Umar Harazumi Da Commissioner II Malan Ali Mustapha Kuraysh da sauran Daraktocin hukumar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...