Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Date:

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka karar da aka shigar game da mayar da Al-Mustapha Jokolo a matsayin Sarkin Gwandu har zuwa ranar 6 ga Yuni.

Kwamitin alkalai biyar karkashin jagorancin Mai Shari’a Uwani Abba-Aji ne ya sanya ranar a ranar Talata bayan da bangarorin da abin ya shafa suka gabatar da takardar hujjoji a kotu.

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

Kwamitin Alkalan ya kuma sanar da cewa duka daukaka kara guda hudu za su bi hukuncin da za a yanke kan daya daga cikin karar.

20250228 181700

A baya, lauyan gwamnatin Jihar Kebbi, Yakubu Maikyau (SAN), ya nemi izinin kotu domin gabatar da karin hujjoji a daukaka karar sa da aka shigar a ranar 19 ga Maris, 2025, kan hukuncin Kotun Daukaka Kara da aka yanke a ranar 14 ga Afrilu, 2016.

Haka kuma, ya jaddada cewa Babbar Kotun Jihar Kebbi ba ta da hurumin sauraron karar da Jokolo ya shigar a ranar 11 ga Disamba, 2014, don haka shari’ar da Kotun Daukaka Kara ta yi ba ta da inganci kuma ba ta da wani tasiri a doka.

Sai dai lauyan Jokolo, Sylvester Imhanobe Esq, ya bukaci kotu da ta yi watsi da karar tare da hukunta Gwamnan Jihar Kebbi, Antoni Janar na Jihar Kebbi, Alhaji Abdullahi Umar, da sauransu da biyan kudaden da suka dace, bisa gazawar su wajen gabatar da hujjojin da za su rushe hukuncin kotunan kasa da suka tabbatar da cewa gwamnan jihar bai gudanar da binciken da ya dace kamar yadda Sashe na 6 na Dokar Sarakuna (Nadin Sarauta da Tsige Sarauta) ta Jihar Kebbi ta tanada kafin tsige Jokolo ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...