Shekarau ya magantu kan batun sake hadewarsu da Kwankwaso

Date:

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekaru ya ce yana da kyakkyawar alaƙa tsakaninsa da da jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

A hirarsa da BBC, Malam Shekarau ya nuna babu wata tattaunawa da nufin sulhu tsakaninsa da Rabiu Musa Kwankwaso, saɓanin rahotannin da ke cewa suna tattaunawa.

Ya ce babu wani sulhu tsakaninsa da jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

InShot 20250115 195118875
Talla

“Ni ban ma yarda a yi amfani da kalmar sulhu ba tsakanina da ɗan’uwana Rabiu Musa Kwankwaso ba.”

“Duk inda ka ji an ce sulhu, to rigima ake yi,” in ji Malam Shekarau.

Malam Ibrahim Shekaru ya ce babu wata matsalar dangantaka tsakaninsa da Kwankwaso.

Sabon Rikici ya Barke Tsakanin Jiga Jigan NNPP Kwankwasiyya a Kano

“Ba na rigama da shi, ba ya rigima da ni, muna gaisawa cikin mutunci da kuma ziyartar juna idan akwai sanadi,” in ji shi.

Tsoffin gwamnonin biyu na Kano Malam shekarau da Rabiu Musa Kwankwaso sun taɓa zama inuwa ɗaya a jam’iyyar APC da kuma NNPP ta Kwankwaso kafin Shekarau ya fice jam’iyyar.

Wasu rahotanni kuma na alaƙanta sasanci ne tsakanin ɓangarorin biyu domin buƙatun siyasa.

Sai dai Shekarau ya ce babu wata tattaunawa ta alaƙar siyasa tsakaninsa.

Ya ce suna tattaunawa tun yana APC da kuma bayan ya fice jam’iyyar Kwankwaso ta NNPP.

Fyade: Kotu ta yankewa wasu mutane 3 hukuncin kisa da yanke musu Mazakuta

“Muna magana da yan’uwantaka da juna tsakanina da Kwankwaso,” in ji Shekarau.

Ya ƙara da cewa babu wata rigima tsakaninsu da har za a yi zancen suna sasantawa tsakaninsu.

Batun sasanci tsakanin tsoffin gwamnonin na Kano biyu ya bijiro ne tun iƙirarin da Sanata AA Zaura ya yi cewa yana ƙoƙarin sasanta su, da kuma tsohon gwamnan Kano kuma shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

2027: Atiku Abubakar ya bayyana matsayarsa game da kasancewarsa a PDP

  Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya musanta rahotannin...

Cikakken Bayani Kan Yan Bindigar da Yansanda Su Ka Kama a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar yansanda ta kasa reshen jihar...

Gidauniyar Sheikh Dr. Muhajihid Aminudden ta rabawa magidanta 600 kayan abinchi a Kano

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Gidauniyar Dr. Muhajihid Aminudden ta rabawa...

Gwamna Abba Gida-gida Ya Kaddamar Da Gyaran Hanyoyi 17 A Babban Birnin Kano

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da...