Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya nada Farfesa Attahiru Jega a matsayin mai ba shi shawara kuma babban jami’in kwamitin bunkasa kiwon dabbobi na Nigeria.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.

Attahiru Jega mai shekaru 68 ya rike mukamin shugaban hukumar zaben Nijeriya daga shekarar 2010 zuwa 2015.
An sake samu tsaiko a shari’ar neman a hana kananan hukumomin Kano kudadensu
Kafin mukamin da Shugaba Tinubu ya ba shi a yammacin Jumma’ar nan, shi ne ya jagoranci kwamitin gyaran kiwon dabbobi da ya bai wa gwamnatin Tinubu shawarar kafa ma’aikata ta musamman don bunkasa kiwon dabbobi wacce yanzu ke da minista.
Sanarwar ta ce ana sa rana Farfesa Attahiru Jega zai yi amfani da gogewar da wajen habbaka harkokin kiwon dabbobi a Nigeria kamar yadda suka bayar da samar da ma’aikata sukutum da guda.