Daga Sani Idris maiwaya
Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji surajo Ibrahim Iman ya kaddamar da rabon takin zamani ga manoma dake yankin dan bunkasa harkar noma.
Alhaji surajo ya bayyana farin cikin dan ganin irin mutanen dake wajen yayin kaddamar da Shirin rabon takin
Shugaban karamar hukumar Dalan ya Hori manoman da su yi aiki da takin ta hanyar da ta dace.

Hon. Surajo Imam ya kuma mika godiyar sa ga gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf bisa takin da ya ba su daga gwamnatin tarayya , inda ya ce takin akwai NPK , UREA da SSP wanda ya kai adadin taki buhu dari takwas da uku (803)
Alhaji surajo imam ya Kara da cewar zasu raba takin daidai da fahimtarsu bisa kungiyoyin da suke yin noma kuma suke da takardarsu ta kungiya a sashen noma na karamar hukumar.
Sanarwar ta musamman daga majalisar limaman masallatan juma’a ta jihar Kano
Cikin wata sanarwa da Jami’ar Yada labaran karamar hukumar Dala Hassana Aminu ta raba Ga manema labarai sanarwar tace a nasa jawabin shugaban sashen noma na yankin Malam sani nano kunya ya taya manoman murnar karbar takin sannan ya yabawa Shugaban karamar hukumar Kan kokarin daya ke na Kawo Cigaba a karamar hukumar.
Daya daga cikin wadanda su ka amfana da wannan rabon takin wakilin hadaddiyarkungiyar Dala small holder farmers malam kabiru nakwango ya yaba da yadda yaga anyi rabon ,sannan ya godewa shugaban karamar hukuma bisa wannan yunkurin na tabbatar da adalci wajen rabon .
Taron ya samu halartar sarkin fadar kano hakimin fagge da hakimin wudil Alhaji sarki ibrahim Alhaji Abdullahi Lamido sanusi da hakimin dala alhaji yahaya inuwa Abbas da Sauran Al’umma gari.