Daga Rukayya Abdullahi Maida
Rashin halartar Lauyan wanda ake kara na 9, Cif Adegboyega Awomolo, SAN a ranar Talata ya kawo cikas ga ci gaban shari’ar da ke neman a dakatar da kudaden kudaden da gwamnatin tarayya ta ke baiwa kananan hukumomi 44 na jihar Kano.
Wadanda suka shigar da karar su ne Abdullahi Abbas, Aminu Aliyu-Tiga, da kuma jam’iyyar APC, ta hannun lauyansu Sunday Olowomoran, inda suka shigar da karar a ranar a ranar 1 ga Nuwamba, 2024.
Kadaura24 ta ruwaito cewa wadanda ake kara a karar sun hada da Babban Bankin Najeriya (CBN), Kwamitin Rabon tattalin arzikin kas (FAAC), da (RMAFC), Akanta-Janar na Tarayya, Ministan Kudi, Auditor Janar na Tarayya, da kuma Ministan shari’a.

Sauran sun hada da Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Gwamnatin Jihar Kano, Kwamishinan shari’a na Kano, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC) da Kananan Hukumomin Kano 44.
Masu kara sun bukaci a rushe zaben kananan hukumomin da aka yi a Kano saboda ba abi ka’idojin dimokuradiyya da kundin tsarin mulkin Nigeria ba.
Sun kuma roki kotun da ta hana Gwamnatin Tarayya da Babban Bankin Najeriya CBN da kuma Babban Akanta Janar baiwa kananan hukumomin Kano 44 na kano kudadensu.
Ta tabbata: NNPC ya sake rage farashin man fetur a Nigeria
A yayin da ake ci gaba da sauraren karar a ranar Talata mai shari’a Simon Amobeda na babbar kotun tarayya da ke Kano, ya sanar da kotun cewa lauyan gwamnatin jihar Kano Awomolo ya aikowa da kotun wasikar neman a dage shari’ar saboda ba ya nan.
Awomolo ya aika da wasika yana neman a dage zaman har sai bayan hutun Ista.
Ba na tunanin an yi adalci idan aka sake dage shari’ar. Saboda an daga shari’ar a lokuta da dama, don haka Bai kamata a daga zaman Kotun ba.
Sanusi Bature ya yabawa Sarki Sanusi II bisa inganta aiyukan yan jaridun fadarsa
“Me ya sa ake son a yi ta jinkirta shari’ar? To Wannan shi ne dagewa ta karshe da zan yi a wannan shari’ar.”
Alkalin ya ba da umarnin a gabatar da dukkan bayanan da suka shafi shari’ar kafin ranar da za a sake zaman shari’ar.
Amobeda ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 14 ga watan Afrilu domin ci gaba da sauraren karar.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito irin haka ta faru a ranar 21 ga Janairu; inda a waccen ranar ma aka nemi a dage shari’ar saboda lauyan KANSIEC John Baiyeshe bai samu halartar zaman ba, saboda dalilai na lafiya kamar yadda ya fada a wata wasika da ya aikawa Kotun.
Tun da farko, lauyan KANSIEC, John Baiyeshea, SAN, ya bukaci kotun da ta dage ci gaba da shari’ar domin yin adalci tunda Awomolo ba ya nan.
Lauyan wanda ya shigar da karar, Abdul Adamu Fagge, SAN, ya kuma bukaci kotun da ta dage ci gaba da shari’ar domin samun adalci.
B. D. Uche, lauyan wanda ake kara na farko; A. Khaleel, lauyan wanda ake kara na uku; da kuma Usman Umar Fari, lauyan kwamishinan shari’a na jihar Kano duk sun bayyana a zaman Kotun.
Solacebase