Gwamnan Kano ya kafa kwamiti domin bincikar dalilin yankewa ma’aikatan albashin

Date:

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya kaddamar da kwamitin da zai gudanar da bincike kan dalilin da yasa aka yankewa ma’aikatan gwamnati a jihar albashinsu na wannan watan.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24 ranar Alhamis.

InShot 20250115 195118875
Talla

Ya bayyana matakin a matsayin cin zarafin ma’aikata wanda ba zai amince da shi ba.

Gwamnan ya sha alwashin fallasawa tare da hukunta wadanda aka samu da hannu wajen aikata hakan.

Ya ce gwamnati ba za ta amince da duk wani zalunci da ake yi wa ma’aikatan ta ba, duk wanda aka samu da hannu a cikin wannan rashin imani tabbas, zai fuskanci fushin doka.

Yadda Ma’aikatan gwamnatin Kano ke kokawa da yankar musu albashin wannan watan

An umurci kwamitin da ya gudanar da cikakken bincike kan albashin jihar daga Oktoba 2024 zuwa Fabrairu 2025, gano ma’aikatan da abin ya shafa, tantance su, tare da ba da shawarar gyara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba za mu lamunci cin zarafi ko tozarta wasu da sunan Tashe ba – Hukumar Hisbah

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Hukumar Hisba ya jihar kano ta...

Da dumi-dumi: El-Rufa’i ya fice daga jam’iyyar APC

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya tabbatar da...

2027: Atiku Abubakar ya bayyana matsayarsa game da kasancewarsa a PDP

  Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya musanta rahotannin...

Cikakken Bayani Kan Yan Bindigar da Yansanda Su Ka Kama a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar yansanda ta kasa reshen jihar...