Da dumi-dumi: Ma’aikatan hukumar samar da ruwa ta Kano sun tsunduma yajin aiki

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano sun tsunduma yajin aiki sakamakon wasu dalilai.

Majiyar Kadaura24 ta Hikima Radio ta rawaito Kafin su tsunduma yajin aikin sai da ma’aikatan suka yi sallah tare da gudanar da alqunuti don Allah kawo musu dauki sakamakon mawuyacin halin da suke ciki.

Sun dai bayyana cewa sun tsunduma yajin aikin ne sakamakon yadda gwamnati ta Kasa fara biyansu mafi karancin albashi na naira 71,000 da gwamnan Kano ya Amince da shi.

InShot 20250115 195118875
Talla

Sun kuma ce bayan kin biyansu mafi karancin albashin, sun akwai ragowar hakkokinsu da suka ce gwamnatin Kano ta gagara biyansu.

Majalisar Limaman Masallatan Juma’a ta bayyana goyon bayanta ga matakin gwamnatin na tantance Kungiyoyin farar hula

Dukkanin kokarin da muka yi na jin ta bakin Manajan Daraktan hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano don jin na su bahasin ya ci tura, Amma za mu cigaba da bibiyar lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ina farin ciki da saukowar farashin kayan abinchi a Nigeria – Tinubu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana...

Yanzu-yanzu: Dangote ya sake rage farashin man fetur

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

APC ta Amince Ganduje ya cigaba da Shugabancinta

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta...

Dalilinmu na rufe wasu hanyoyi a Kano – Rundunar yansanda

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta...