Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Jam’iyyar NNPP reshen Kano ta dakatar da wasu manyan mambobin ya hudu da suka hada da Sanata Kawu Sumaila, Ali Madakin Gini, Sani Abdullahi Rogo, da Kabiru Alhassa Rurum, bisa zarginsu da yiwa jam’iyyar zagon kasa.
Kadaura24 ta rawaito Shugaban jam’iyyar na jihar Kano Hashimu Suleiman Dungurawa ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.
A cewar Dungurawa, an zabi wadannan ‘yan majalisar dokokin ne a karkashin jam’iyyar NNPP amma a kwanakin baya suna yin wasu abubuwa da suka saba da Manufofi da akidar jam’iyyar.

Ya ce an ba su tikitin takara a jam’iyyar gabanin zabukan da suka gabata, amma maimakon su nuna godiya, sai suke yin abubuwan da suka ci karo da muradun jam’iyyar.
Wani lamari na baya-bayan nan da ya janyo dakatarwar shi ne yadda aka gudanar da daurin auren diyar Sanata Kawu Sumaila da kuma bikin yaye ɗaliban jami’ar kawu Sumaila.
Dungurawa ya bayyana mamakinsa da cewa wadanda suka halarci taron galibinsu mutane ne da su ka yaki Kawu a baya, amma kuma ya gayyatosu harkarsa kuma ya ki gayyatar ‘yan jam’iyya NNPP.
Sabon Rikici Ya Kunno Kai Cikin Jam’iyyar APC a Kano
Shugaban jam’iyyar ya bayyana cewa za a kafa kwamitin da zai binciki lamarin tare da sanar da al’umma sakamakon karshe da jam’iyyar za ta dauka.
Duk da dakatarwar, Dungurawa ya jaddada cewa har yanzu akwai sauran damar tattaunawa ga wadanda aka dakatar din, idan har suka nemi afuwa jam’iyyar za ta iya yafe musu.