Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Shugaban jam’iyyar NNPP mai kayan marmari ta jihar Kano Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa ya ce Sanata Kawu Sumaila da yan Majalisun tarayya da yan Kwankwasiyya suka yi da’awar korar su ba su koru daga jam’iyyar ba.
“Shi wanda ya yi korar ba shi da hurumin yin korar, saboda ba ya daga cikin Shugabanni don haka shi Sanata Kawu Sumaila da Kabiru Alhasan Rurum da Ali Madakin gini da Abdullahi Sani Roga suna nan a jam’iyyar NNPP ba su koru ba”.
Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a Kano.

Ya ce shi ne halastaccin shugaban jam’iyyar NNPP na Kano don haka shi ne yake da hurumin kora ko dakatar da wani daga jam’iyyar ba wani daban ba.
“A ka’ida da kundin tsarin mulkin jam’iyyar NNPP ba wanda ya isa ya kora do ya dakatar da wanda ya ke mamba ne na majalisar kolin jam’iyyar NNPP, ballantana kuma wanda ya ke ba shugaban ba”. Inji Doguwa
Yanzu-yanzu: NNPP ta dakatar da Sanata Kawu Sumaila da wasu yan Majalisar wakilai a Kano
Sanata Doguwa ya ce a sanin sa jam’iyyar NNPP ta Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, sannan kuma ta dakatar da Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar .
Yayin da yake jawabin, shugaban jam’iyyar NNPP mai kayan marmari sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa ya nunawa yan jarida takardar shaidar shi ne sahihin shugaban jam’iyyar, sannan ya nuna hukuncin kotu da yake tabbatar da cewa jam’iyyar NNPP mai kayan marmari ita ce ingantacciyar jam’iyya ba mai littafi ba.